✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin tsaro: ‘Sai an yi wa Buhari addu’a’

Buni ya ce sai ’yan Najeriya sun hada wa Buhari da addu'a kan samar da tsaro.

Shugaba Buhari na bukatar taimakon ’yan Najeriya domin samun nasara a kokarinsa na samar da tsaro a kasar.

Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ne ya bayyana haka, yana mai kira ga ’yan kasar da su taimaka wa Shugaban Kasar wajen kawo karshen matsalolin tsaron da suka dabaibaye Najeriya.

Buni ya kara da roko tare da jaddada muhimmancin addu’ar ’yan kasa domin Allah Ya kawo wa Najeriya aminci da cikakken tsaro.

Ya yi rokon ne a yayin zantawa da ’yan jarida bayan saukowa daga sallar idi, a Damaturu, hedikwatar Jihar Yobe.

Gwamnan wanda shi ne Shugaban Riko na Jam’iyyar APC ya kuma tabbatar da cikakken goyon bayansa da Shugaba Buhari da kokarinsa na ganin bayan ayyukan ta’addanci da ke barazana ga dorewar Najeriya.