✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rashin tsaro ya rage mana kudin shiga daga man fetur – Buhari

Ya bayyana hakam ne a Jihar Imo

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dora alhakin karancin kudin shiga a lalitar Gwamnatin Tarayya daga albarkatun man fetur a kan matsalar tsaro.

Shugaban ya bayyana hakan ne a Owerri babban birnin jihar Imo a jawabinsa ga masu ruwa da tsaki da suka taru a gidan gwamnatin jihar a ranar Talata.

Buhari ya ce gwamnatinsa ta tunkari matsalar kuma tana samun nasarar maganceta. 

Sai dai takaicinsa shi ne yadda wasu ke daure wa musu aikata wannan barna gindi a kasar nan.

Shugaban ya ce, “Ku dubi yadda muhimman kayayyakin bukatu da gwamnatin ta samar ke lalacewa, ku duba yadda aka kashe jirgin kasa, haka wutar lantarki inda muke fama da matsala.”

 Buhari ya koka da yadda farashin danyen man fetur ya fadi daga Dala 28 zuwa 27 wanda ya rage wa gwamnati kudin shiga.

Sai dai duk da haka a cewarsa gwamnatinsa ta yi rawar gani wajen magance wadannan matsalolin.

Buhari ya ce, ya yi wadannan maganganu na na yabo kai ne, saboda wadanda ya kamata su yaba ba su yaba ba, bai kuma san dalilin da ya sa suka rufe bakinsu ba kan wannan cigaba na gwamntinsa ba.

Daga karshe Buhari ya yi kira ga manyan kasar nan da su hada hannu da gwamnatinsa a yaki ta’addanci da kuma sauran matsalolin tsaro da su ka addabi kasar nan.