✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rasuwar Bouteflika: Ra’ayoyi sun bambanta a Algeria

Wasu 'yan Algeria nacewa za a tuna da Bouteflika, wasu kuwa sun ce ba za su yi kewa ba

Ra’ayoyin ’yan Algeria sun bambanta game da rasuwar tsohon shugaban kasar, Abdelaziz Bouteflika, mutumin da ya shafe shekara 20 yana mulki.

Ya rasu ne dai yana da shekara 84 a duniya, kuma ranar Lahadi za yi jana’izarsa.

Tsohon shugaban na Algeria ya sauka daga Mulki ne a watan Afrilun 2019 bayan sojoji sun juya mishi baya a yunkurin da ya yi na tsayawa takara don neman wa’adin mulki na biyar a jere sakamakon gagarumar zanga-zangar adawa da al’ummar kasar suka yi makwanni suna yi.

Tun daga lokacin aka daina ganin shi a bainar jama’a saboda kebewa da ya yi a wani gidansa da ke yammacin Algeria.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa sanarwar rasuwarsa a daren Juma’a ta haddasa alhini a fadin kasar, mai yiwuwa saboda rashin ganin shin a tsawon lokaci.

Ya bar tarihi

Wata sanarwa daga magajinsa, Abdelmadjid Tebboune, ta hakaito tarihin rawar da Bouteflika ya taka yayin yakin kwatar ’yanci daga Faransa, sannan ta ce za a saukar da tutocin kasar har tsawon kwana uku don karrama shi.

A cewar Mansour Kedidir, wani masanin harkokin siyasa, “ta fuskoki da dama Abdelaziz Bouteflika ya shiga kundin tarihin Algeria tun daga lokacin da aka samu mulkin kai.

“Za a rika tunawa da shi duk da abin da masu suka za su fada”.

Sai dai da dama daga cikin mazauna Algiers, babban birnin kasar, sun shaida wa AFP cewa ba za su yi kewar Bouteflika ba.

“Allah Ya jikan shi, amma bai cancanci yabo ba saboda ba abin da ya tsinana wa kasar nan”, inji wani mai kayan miya, Rabah.

Gidan talabijin na kasar ya ce ranar Lahadi za a binne Bouteflika a makabartar El-Alia da ke gabashin Algiers, inda aka binne wadanda suka gabace shi da sauran wadanda suka kwanta dama a yakin kwatar ’yancin kasar.

Alamu sun nuna cewa ana shirye-shiryen ajiye gawarsa a Fadar Al’umma ta kasar kafin a yi mishi jana’iza.

Mai takalmin karfe

Bouteflika ya zama shugaban kasar Algeria ne a 1999 bayan yakin basasa a tsakanin masu kishin Musulunci da sojoji wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 200,000.

Bayan nan ya lashe zabuka don yin wa’adin mulki na shekara biyar har sau uku, na karshen a 2014.

Kimarsa ta karu a idon al’ummar kasar, wadanda suke yi mishi lakabi da Boutef, lokacin da ya rike mukamin Ministan Harkokin Waje a shekarun 1970, da kuma rawar da ya taka wajen samar da zaman lafiya bayan yakin basasar, musamman wata dokar afuwa da ta karfafa wa dubban masu kishin Musulunci gwiwa su mika makamansu.

Farid Alilat, wani dan jarida da ya rubuta tarihin Bouteflika, ya ce daukacin madafun iko suna hannun tsohon shugaban, kuma yana samun goyon bayan rundunar sojin kasa da jami’an leken asiri lokacin da yake kan ganiyarsa a shekarun 2000.

“A lokacin ya zama shugaban kasa mai takalmin karfe”, inji Alilat.

In ban da abin da ba a rasa ba, juyin juya halin da ya watsu a kasashen Larabawa a 2011 bai yi tasiri ba a Algeria.

Mutane da dama na alakanta hakan da kudar da aka sha a lokacin yakin basasa da kuma ihsanin da gwamnati ke raba wa jama’a.

Amma cin hanci da rashawa sun yi katutu a mulkin Bouteflika, lamarin da ya sa ’yan Algeria da dama mamakin yadda kasa mai dimbin albarkatun man fetur ta wayi gari babu ababen more rayuwa ga kuma tsananin rashin aikin yi da ya tilsata matasa barin kasar.

Rashin lafiya

A shekarun karshe na mulkinsa, jinya ta fara cin karfin Bouteflika, lamarin da ya sa ya rasa kima a matsayinsa na shugaban kasa.

Duk da ciwon zuciyar da ya buge shi a watan Afrilun 2013 ya shafi furucinsa ya kuma tilasta mishi amfani da keken guragu, ya yanke shawarar tsayawa takara don neman wani sabon wa’adin mulki a karo na hudu.

Yunkurinsa na neman wa’adi na biyar a 2019 ya fusata al’ummar kasar ya kuma haddasa zanga-zangar da ta rikide ta zama guguwar neman kafuwar dimokuradiyya wadda ake kira “Hirak”.

Dole ya sauka daga mulki lokacin da sojoji suka juya mishi baya.

Zanga-zangar Hirak

Duk da haka an ci gaba da zanga-zangar Hirak tare da kira da a yi wa tsarin mulkin kasar, wanda aka shimfida shi tun lokacin da aka samu ’yanci daga Faransa a 1962, cikakken garambawul

Daga bisani dai an daure wasu manyan jami’ai na zamanin Bouteflika bayan samunsu da laifin almundahana, ciki har da dan uwansa Said wanda a baya mai karfin fada-a-ji ne.

A karshen 2019 aka zabi magajin Bouteflika, Tebboune, a wani zabe da ba a taba samun rashin fitar masu kada kuri’a kamarsa ba, bayan da masu zanga-zangar Hirak suka yi kira da a kaurace.

Annobar coronavirus ce dai ta tilasta jingine zanga-zangar ta Hirak, wadda ta ke ta tangal-tangal a yunkurinta na sake farfadowa yayin da gwamnati ke kamen ’yan adawa.