✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rayuka sun salwanta a rikicin sojoji da direbobin haya a Jihar Kwara

Akalla fararen hula biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon wata mummunar arangama da ta auku tsakanin wasu sojoji da direbobin motocin haya a yankin Ilesha-Baruba…

Akalla fararen hula biyar ne suka rasa rayukansu sakamakon wata mummunar arangama da ta auku tsakanin wasu sojoji da direbobin motocin haya a yankin Ilesha-Baruba da ke Karamar Hukumar Baruten a Jihar Kwara.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa ruguntsimin ya auku ne a ranar Juma’ar da ta gabata sakamakon wata rashin jituwa da ta auku tsakanin direbobin da kuma sojojin da suka sanya shingen bincike a kan hanyar ta Chikanda da matafiya suka saba bi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, wani direba da ke kan hanyarsa ta dawo wa daga kasuwar Sinawu ne ya hau kujerar naki ta biyan Naira dari biyu da sojojin suka nema a wurinsa.

An ruwaito cewa direban ya shaida wa sojojin cewa ya riga da ya biya kudin tun a baya da sanyin safiya, amma hakan ya fusata sojojin inda suka shiga ladabtar da shi ta hanyar mari da sanya shi tsallen kwado baya ga motarsa da suka kwace.

Bayan direban ya gama diban gajiyar da sojojin suka tara masa ne ya kai korafi wajen kungiyarsu ta masu motocin haya.

NAN ya ruwaito cewa, neman jin bahasin lamarin a wurin sojojin da ‘yan kungiyar suka yi yunkuri a madadin direban ne ya sanya aka shiga cacar baki inda kuma daga nan aka tayar da kura babu ji babu gani da har ta kai an harbe mutum uku nan take suka mutu yayin da daga bisani wasu biyun suka mutu a sakamakon rauni na harbin bindiga.

Wata majiyar rahoton ta ce an killace gawar wadanda suka riga mu gidan gaskiya a dakin ajiyar gawawwaki a Asibitin Saki da ke Jihar Oyo.

Ta kara da cewa sauran wadanda suka jikkata a yayin hargitsin na ci gaba da samun kulawa ta kwararru na lafiya a Asibitin na Saki yayin da wasunsu kuma aka garzaya da su wajen masu bayar da maganin gargajiya a kauyen Kenu domin a zare harsashin bindigar da ke jikinsu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa tarzomar ta lafa sai dai ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano ainihin asarar da aka samu.