✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rayukan ’yan Najeriya ba su dami Buhari da gwamnonin Arewa ba —ACF

ACF ta ce halin ko-in-kula da Buhari da gwamnonin suke nunawa ya tabbatar cewa rayukan iyalansu da ofisoshinsu ne suka fi damun su.

Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin jihohin Arewa 19 sun nuna wa ’yan Arewa cewa rayukan mutanen yankin bai dame su ba.

ACF ta ce irin halin ko-in-kula da Buhari da gwamnonin suke nunawa ya tabbatar cewa rayukan iyalansu da kuma ofisoshinsu ne suka fi damun su.

“A wannan halin ha’ula’in rashin tsaro da ake ciki a Arewa babu abin da za a ce ya hana Shugaban Kasa da gwamnoni kai ziyarar jaje a wuraren da wadannan abubuwa ke faruwa.

“Abin bakin ciki ne yadda Shugaban Kasa bai ga dacewar yin hakan ba; Gwamnoni kuma suka yi koyi da shi, in banda Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno kadai,” inji sanarwar kungiyar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a yayin da take nuna alhininta kan kazamin harin da ’yan bindiga suka kai a mazabar Idasu ta Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, inda suka kashe mutum 40, da sauran makamantansa a sassan Arewacin Najeriya.

Ta kara da cewa, “An kai irin harin a Uba Askira na Jihar Borno inda aka kashe mutum 10 aka sace wasu da dama. Amma gwamnonin Arewa da Shugaban Kasa suna nuna wa mutanen da hakan ke faruwa da su cewa ba su damu da rayuwarsu ba. ACF ta yi amannar cewa hakan ba girman Shugaban Kasa da gwamnonin Arewa ba ne.”

Ta bukaci Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gaggauta ziyartar kauyukan da aka kai wa hari a Giwa domin jajanta wa al’ummar yankin.

A cewarta, wajibi ne gwamnan da Shugaba Buhari su tausaya wa al’umma tare da nuna musu kulawa a yayin da ake fama da wannan yanayi na tabarbarewar tsaro.

An kai harin na Giwa ne a ranar Asabar da yamma, washegari Lahadi kuma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo Najeriya daga ziyarar aiki da ya kai kasar Turkiyya.

Kwanaki kadan kafin tafiyarsa zuwa Turkiyya, Buhari ya sha suka kan halartar taron kaddamar da littafin tarihin jigon jam’iyyar APC kuma tsohon Gwamnan Jihar Osun, Cif Bisi Akande, a Legas, jim kadan bayan harin da ’yan bindiga suka yi wa matafiya kisan gilla a Jihar Sakkwato, ba tare da ya je ta’aziyya ba.

Bayan sukar, ya tura tawagar manyan jami’an tsaro zuwa Sakkwato domin yin ta’aziyya da kuma Jihar Katsina inda aka kashe Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na jihar.

Kawo yanzu dai Kungiyar Gwamnonin Arewa karkashin jagorancin Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato ba ta ce uffan ba tukuna kan takardar ta ACF.

Wakilinmu ya kira Daraktan Yada Labaran Lalong, wato Makut Simon Macham, ta waya, ya kuma tura masa rubutaccen sakon neman jin ta bangarensu, amma har muka kammala hada wannan rahoto, bai amsa ba.

Fadar Shugaban Kasa ta yi gum

Ko da yake sa’o’i kadan kafin fitowar sanarwar ta ACF, kungiyar gwamnonin ta hannun Lalong ta bayyana gamsuwarsu da hare-haren da sojoji ke kai wa ’yan bindiga da ’yan ta’adda da suka addabi yankin. 

Sanarwar ta ce, “Muna so a ci gaba da hakan da alkibla daya a lokaci guda ta yadda ’yan ta’addan ba za su iya sauya maboya ba bayan an fatattake su daga wani wuri.”

A cewarsa, hakan ne zai tabbatar da murkushe su gaba daya tare da hana su sake taruwa, saboda tabbatar da doka da oda a fadin Najeriya.

Ta kuma yi tir da hare-haren baya da aka kai a kananan hukumomin Jihar Kaduna, Wase a Jihar Filato, Askira Uba da sauran kananan hukumomin Jihar Borno, da Neja da sauransu wuraren da aka kashe mutane da ba su ji ba, ba su gani ba. 

Daga Sagir Kano Saleh, Umar Muhammed (Lafia), Lami Sadiq (Kaduna) da Dickson Adama (Jos)