✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rayuwar dana kamar ta kowane dan Najeriya ce —Sanata Na’Allah

Sanatan ya ce ya bar komai a hannun Allah madaukakin sarki.

Sanata Bala Ibn Na’Allah ya ce rayuwar dansa Abdulkarin da aka yi kisan gilla daidai take da ta kowane dan Najeriya.

Sanata Na’Allah wanda ba ya Najeriya lokacin da labarin mutuwar dan nasa ta riske shi, ya ce yana fata kashe dan nasa da aka yi zai bude kofar shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.

A cikin wata sanarwa, Sanatan ya  ce wadanda suka kashe dan nasa sun shiga gidansa ne ta saman rufin gidan suka kashe shi.

“Rayuwarsa ba ta da wani bambanci da rayuwar kowane dan Najeriya. A matsayinmu na iyayensa mun bar komai a hannun Allah, sannan mun gode bisa yadda jama’a ke aiko da sakonnin jaje da ta’aziyya,” a cewarsa.

Sanata Na’Allah wanda ke wakiltar Kebbi ta Kudu ya ce, “Muna tabbatar wa jama’a cewa yadda aka kashe shi abun ya yi muni, amma za mu ci gaba da mika komai ga Allah.

“Muna fatan a matsayinmu na iyayen kasa za mu nemo mafita game da matsalar tsaro a wannan kasa.”

A cewarsa, Abdulkarim duk da cewa Abdulkarim ya koma ga Mahallicinsa, ba za su gushe suna kaunar sa ba da kuma yi masa addu’ar samun rahama da Aljanna Firdausi.

Ya gode wa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da kuma Gwamnatin Jihar Kaduna kan kokarinsu a kan lamarin.

Aminiya ta rawaito cewa an kashe babban dan na Sanata Na’Allah, wanda aka samu gawarsa a gidansa da ke titin Umaru Gwandu a unguwar Malali a garin Kaduna.