✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta ci kwallo 1,000 a gasar Zakarun Turai

Real Madrid ta ci kwallo 1,000 rigis a gasar Zakarun Turai.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta zama ta farko a tarihi da ta zura kwallaye har 1,000 a koma a gasar Zakarun Turai watau Champions League.

Real Madrid ta hau kan wannan kadami ne a nasarar da ta yi na doke Shakhtar Donetsk 2-1 a wasa na a wasa na hudu kuma rukuni na hudu da suka fafata a ranar Laraba.

A minti na 14 da fara wasan ne Karim Benzema ya jefa wa Real Madrid kwallon farko kuma cikon ta 1,000 ke nan da kungiyar ta ci a tarihi.

A daidai minti na 39 sauran minti shida a tafi hutun rabin lokaci ne Shakhtar ta farke wannan kwallo ta hannun dan wasanta, Fernando.

Bayan an dawo hutun rabin lokaci ne Karim Benzema ya kara na biyu a minti na 61 na karawar da hakan ya sa kungiyar Sifaniya ta ci gaba da jan ragamar teburi na hudu.

Kwallaye biyun da dan wasan na Faransa ya zura a wasan su ne suka bai wa Madrid damar zama kungiya ta farko da ta kafa sabon tarihin na cin kwallo sama da 1,000 ke nan a tarihin Gasar Zakarun Turai.

Kungiyar Bayern Munich ta kasar Jamus ce ke biye wa Madrid a yawan cin kwallaye a gasar da kwallo 768, yayin da abokin hamayyarta, Barcelona ke matsayi na uku da kwallaye 655.

Kungiyar Manchester United wadda tsohon dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya koma, ce ke cikon ta hudu a yawan cin kwallayen da kwallo 529.

Real Madrid ta yi fitattun ’yan wasa da dama zakakuran cin kwallaye a tsawon shekaru 119 da ta shafe na kafuwarta, sai dai duk cikinsu babu wanda Cristiano Ronaldo bai yi wa fintinkau da zarra ba a tsawon shekaru 9 kacal da ya shafe tare da kungiyar.

Alkalumma sun tabbatar cewa Cristiano Ronaldo ya sha gaban duk wani dan kwallo a raye ko a mace wajen yawan zura kwallaye a koma.

Ronaldo wanda kuma shi ne dan wasa mafi yawan zura kwallaye a tarihin gasar Zakarun Turai, shi ne dan Real Madrid mafi zura kwallaye a tarihinta wanda yake da kwallaye 105 da ya ci mata a gasar ta Zakarun Turai kadai.

Ga jerin wadanda suka yi wa Real Madrid bajintar kafa tarihin a gasar Zakarun Turai:

Miguel Munoz ne ya fara ci wa Real Madrid kwallon farko a European Cup, bayan da ta doke Servette a waje da ci 2-0 a karawar zagayen kungiyoyi 16.

A kaka hudu tsakani, Alfredo Di Stefano ya zura kwallo na 100 a fafatawar daf da karshe a gida da Real ta yi nasara a kan Barcelona da ci 3-1.

Shi kuwa Ferenc Puskas ya zura kwallo na 200 a Real Madrid a wasan da ta doke Feyenood da ci 5-0 a zagayen kungiyoyi 32 a 1965/66.

An ci kwallo na 300 a Real Madrid a gasar Zakarun Turai a kaka ta 13, inda Jensen ya zura na biyu a raga a 7-0 da ta yi nasara a gidan Progress Niedercorn.

Kwallo na 400 kuwa a kakarr 1990/91 aka zura a raga, bayan da Sebastián Losada ya ci a wasan da Real ta tashi 2-2 da Swarovski Tirol.

Guti ne ya zura na 500 a raga a wasan da Real Madrid ta doke Sporting 4-0 a karni na 20 a fafatawar cikin rukuni a kakar 2000/01.

David Beckham ne ya ci na 600 a wasan da Real ta doke Marseille 2-1, yayin da Gonzalo Higuaín ya zura na 700 a raga a karawar da Real Madrid ta tashi 2-2 da AC Milan a 2010.

Kyaftin din tawagar Portugal, watau Cristiano Ronaldon dai shi ne ya ci na 800 a wasannin cikin rukuni da Real Madrid ta yi nasara a kan Copenhagen a waje da ci 2-0 a karshen kakar 2013.

Ronaldo ne ya ci na 900 a 2017 a fafatawa da Bayern Munich wasa na biyu a zagayen ’yan da suka tashi 4-2.

Shekara hudu ke nan a tsakani da Karim Benzema ya ci na 1,000 a karawa da Shakhtar ranar Laraba 3 ga watan Nuwambar 2021.