✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta doke Athletic Bilbao babu ’yan wasa 11

Madrid ta yi nasarar duk da rashin manyan ’yan wasanta 11 a fafatawar

Real Madrid ta doke Athletic Bilbao har gida da ci 1-2 a ranar Laraba ba tare sa manyan ’yan wasanta 11 ba, sakamakon kamuwa da COVID-19.

Real Madrid ta fara zura kwallo ne a minti na 4 ta hannun dan wasan gabanta Benzema, wanda ya sake karawa a minti na 7.

A minti na 10 ne dan wasan gaban Athletic Bilbao, Sanchet ya farke kwallo daya, wanda a haka aka tashi daga wasan.

Madrid ta ziyarci filin wasa na San Mames da ke birnin Bilbao ne ba tare da ’yan wasa irin su Rodrygo, Asensio, Alaba, Marcelo, Modric, Bale, Lunin, Isco, sakamakon gwajin cutar COVID-19 da ya nuna sun kamu da ita.

Carvajal ya samu rauni, shi kuma Casemiro bai buga wasan ba saboda samun katin gargadi da yawa, Dani Ceballos kuma na murmurewa daga raunin da ya samu.

Real Madrid ta ci gaba da jan ragamar teburin Gasar Laliga na kasar Spain, inda ta ba wa Sevilla da ke ta biyu tazarar maki takwas.