✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Real Madrid ta kai bantenta a Super Cup na Sifaniya

Courtois ne ya ceci Real Madrid a bugun fanareti.

Real Madrid ta samu nasarar kai bantenta zuwa wasan karshe na Kofin Zakaran-Zakaru na Sifaniya, wato Spanish Super Cup.

A ranar Laraba ce Real Madrid dai ta doke Valencia a bugun fanareti a wasan kusa da karshe na kofin a karawar da aka yi a filin wasa na Sarki Fahd da ke babban birnin Saudi Arabia, Riyadh.

Karim Benzema ne ya fara sakada kwallo a ragar Valencia a bugun fanareti ana tsaka da wasan inda zakarun na Turai da kuma La Liga suka kasance a gaba.

Sai dai kuma Samuel Lino ya farke kwallon jim kadan da komawa fili daga hutun rabin lokaci, wasan ya kasance 1-1.

Hakan ne ya sa aka tafi bugun fanareti a karshen wasan inda Madrid ta yi nasara da ci 4-3.

Madrid ta ci dukkanin bugunta, yayin da Eray Comert ya barar da tashi, kuma mai tsaron raga Thibaut Courtois ya tare ta Jose Gaya.

Bayan wasan Courtois ya yi bayani kan yadda ya samu nasarar taka wa Valencia birki a bugun na fanareti.

Ya ce, “ba shakka dole ne a matsayinka na mai tsaron raga ka yi nazari a kan fanareti.

“Gaya ya barar da bugun da ya yi na karshe a wasansu da Sevilla ta hannun hagu, sannan ya ci bugunsa na karshe ta tsakiya a karawarsu da Betis, to ka ga mun san nan zai nemi ya sake bugawa,’’ In ji Courtois.

A ranar Alhamis din nan ne Real Betis za ta kara da Barcelona a daya wasan na kusa da karshe na gasar ta Spanish Super Cup, kuma duk wadda ta yi nasara za ta hadu da Real Madrid a wasan karshe a birnin na Riyadh da ke Saudiyya.

Nasarar lashe kofin na Spanish Super Cup da Real Madrid ta yi bayan lallasa Atletico Bilbao a wasan karshe na kakar da ta gabata ya nuna cewa tana da irin kofin har guda 12 — banbancin guda daya tal tsakaninta da Barcelona wadda ke da tarihin dage kofin sau 13.

Ita dai gasar wannan kofi da ake kira Supercopa de España a yaran Sifaniya, ana buga ta ne tsakanin kungiyoyi hudu da suka hada da kungiyoyin da suka lashe gasar La Liga, Copa del Ray da kuma kungiyoyin da suka zo na biyu a gasannin biyu.