✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Real Madrid ta lashe kofin UEFA Super Cup na 5

Madrid ta lasje kofin sau biyar a tarihinta.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta sake zama zakara, bayan doke Frankfurt da 2 – 0 a wasan karshe na gasar UEFA Super Cup.

Ana buga kofin Super Cup ne a tsakanin kungiyoyin da suka lashe kofin Gasar Zakarun Turai da na UEFA Europa League.

Madrid ce ta fara zura kwallo a minti na 37 ta hannun dan wasanta David Alaba, kafin tafiya hutun rabi lokaci.

Bayan dawowa daga hutun rabi, zakaran Real Madrid, Benzema ya kara kwallo ta biyu a minti 65.

Real Madrid ta lashe kofin Super Cup sau biyar a tarihi.