✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta lashe Kofin Zakarun Turai karo na 14

Real Madrid ta sake kafa tarihi bayan doke Liverpool da ci daya mai ban haushi.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta doke Liverpool da ci daya mai ban haushi a wasan karshe na gasar Zakarun Turai.

Wannan shi ne karo na 14 da kungiyar ke lashe gasar a tarihinta.

Liverpool da Real Madrid sun shafe tsawon minti 95 suna gumurzu wanda daga karshe aka ware tsakanin zare da abawa.

Dan wasan gaban Real Madrid, Vinicius Junior ne ya zura kwallo daya tilo a ragar Liverpool a minti na 59.

Real Madrid ce kadai ta taba lashe gasar sai 14 a tarihi, sai AC Milan da ke da guda bakwai, yayin da Liverpool ta ke da guda shida.

Bayern Munich ita ma tana da guda shida, Barcelona na da guda biyar, Ajax na da hudu, Manchester United da Inter Milan kowane na da guda uku kowannensu.

Wadanda suka taba lashe gasar sau biyu kuwa su ne; Juventus, Benfica, Chelsea, Nottingham Forest da kuma FC Porto.

Dan wasan gaba na Real Madrid, Karim Benzema ne ya fi kowane dan wasa zura kwallo a raga a gasar, inda yake kwallaye 15.

Sai dan wasan gaban Bayern Munich wato Robert Lewandowski da ke biye masa da kwallaye 13.

A baya Real Madrid ta taba yin shekara uku a jere tana lashe Gasar Zakarun Turai.