✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid ta mika tayin sayen Kylian Mbappe

Mbappe ya ki amincewa da tayin tsawaita yarjejeniyarsa da PSG har sau 3.

Real Madrid ta mika tayin yuro miliyan 160 don sayen dan wasan gaban Paris Saint Germain, Kylian Mbappe na kasar Faransa.

Fitaccen dan jarida wanda kuma ya shahara a kan fashin baki da tattara bayanan lamurran da suka shafi sauyin shekar ’yan wasa, Fabrizio Romano dan kasar Italiya ne ya tabbatar da tayin na Real kan Mbappe a shafinsa na twitter a daren ranar Talata.

Romano wanda ke da mabiya da suka zarta miliyan hudu a shafinsa na Twitter, ya ce a na shi bangaren, Mbappe ya ki amincewa da tayin tsawaita yarjejeniyarsa da PSG har sau 3, saboda sauyin shekar da ya dage yana bukata.

Dan wasan mai shekara 22 da ya lashe Kofin Duniya, ya koma PSG a 2017 kan kudin da suka kai fan miliyan 165 wanda kuma yarjejeniyarsa za ta zo karshe a watan Yunin 2022.

Real Madrid wadda ake bi bashin da ya kai kusan fan biliyan daya, David Alaba kadai ta dauka a wannan kakar daga Bayern Munich kuma kyauta.

Ganin cewa Sergio Ramos da Raphael Varane wadanda ke daukar albashi mai yawa sun bar kungiyar, Real na ganin za ta iya sayo Mbappe ba tare da ta fuskanci wata matsalar kudi ba.

A halin yanzu babu cikakken bayani kan yadda za a tsara biyan kudin sannan kuma har yanzu PSG ba ta ce komai kan tayin ba tukunna.

Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa, PSG ta yi watsi da tayin yuro miliyan 160 da Real Madrid ta yi mata kan neman kulla yarjejeniya da tauraronta Kylian Mbappe.

Yanzu haka dai kasa da shekara daya ya rage wa yarjejeniyar Mbappe da PSG ta kare.

Mbappe ya ci wa PSG kwallaye 92 cikin wasanni 110 da ya buga mata, tun lokacin da ya koma kungiyar daga Monaco a matsayin aro a shekarar 2017 kafin daga bisani su kulla yarjejeniyar dindindin.

Mbappe da ke zaman na uku a jerin yan wasa mafi yawan kwallaye a PSG, ya lashe kofin gasar Ligue 1 uku da French Cup uku.