✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Real Madrid za ta dawo da zawarcin Cavani, Chelsea ta cije a kan Rudiger

Chelsea na son Antonio Rudiger ya kulla sabon kwantaragi da ita.

Chelsea ta ci gaba da tattaunawa da wakilin dan wasan bayanta na kasar Jamus, Antonio Rudiger mai shekara 28, kan sabon kwantaragi. (Fabrizio Romano via Twitter)

Ta yi wu Arsenal ta sanya hannu kan dauko sabon mai tsaron raga a kakar da muke ciki, sai dai tana duba yiwuwar dauko Golan Jamus, Bernd Leno mai shekara 29. (Metro)

Akwai yiwuwar Real Madrid za su dawo da zawarcin da suke yi wa dan wasan gaban Manchester United da Uruguay, Edinson Cavani mai shekara 34, idan aka bude kasuwar saye da sayar da ’yan wasa a watan Janairun badi. (El Nacional)

Barcelona ta jingine shawarar sallamar kocinta, Ronald Koeman na kasar Holland, gabanin wasan La Liga da za ta kara da Atletico Madrid a ranar Lahadi. (Sport)

A yanzu haka dai an sanya sunan kocin Liverpool dan kasar Jamus, Jurgen Klopp da ake kyautata zaton zai maye Koeman (El Nacional)

Haka kuma ana duba yiwuwar dauko tsohon kocin Juventus, Andrea Pirlo da kocin River Plate, Marcelo Gallardo, wadanda duk a shirye suke su shiga Nou Camp.

Kocin Liverpool, Jurgen Klopp na sha’awar dauko dan wasan Bayern Leverkusen, Moussa Diaby na kasar Faransa mai shekara 22. (Caliciomercato)