✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rigakafin COVID-19 miliyan 1 ya lalace a Najeriya kafin a yi amfani da shi – Bincike

Binciken ya kuma gano cewa an kawo rigakafin ne yana dab da lalacewa.

Wani bincike ya gano cewa kimanin rigakafin COVID-19 samfurin AstraZeneca miliyan daya ne ya lalace a Najeriya a watan Nuwamba ba tare da an yi amfani da shi ba.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wani bincike da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa a ranar Laraba, inda ya ce hakan na nuni da kalubalen da kasashen Afrika ke fuskanta wajen yaki da annobar ta COVID-19.

Ana dai ganin wannan a matsayin daya daga cikin asara mafi grima da aka taba tafakawa a lokaci daya a kowace kasa a fadin duniya.

Binciken ya kuma gano cewa wuraren da aka ajiye rigakafin da kuma karancinsa, da kasancewar an kawo shi Najeriya yana dab da daina aiki, sun taka muhimmiyar rawa wajen lalacewarsa kafin amfanin.

Najeriya dai na da mutane sama da miliyan 200, amma kasa da kaso hudu cikin 100 ne aka yi musu rigakafin cutar, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tabbatar.

A cewar binciken, kamfanin AstraZeneca ne ya sarrafa rigakafin, kuma an kawo shi ne daga Turai, ta hanyar tallafin da hadakar kasahe ke ba wa kasashe masu karamin karfi.

Wata majiya ta shaida cewa wasu daga cikin rigakafin an kawo su ne mako hudu zuwa shida kafin lokacin lalacewarsu, kuma ba za a iya amfani da su kafin lokacin ba.

Majiyar ta kara da cewa har yanzu dai ana ci gaba da kidaya lalatattun rigakafin, kafin a fitar da hakikanin adadinu nan gaba.

Kakakin Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Kasa, (NPHCDA), ya ce har yanzu hukumar na ci gaba da tattara alkaluman raigakafin da aka shigo da su da wanda aka yi amfani da su kafin ta fitar da alkaluma a nan gaba kadan.

WHO dai ta tabbatar da lalacewar rigakafin, amma ba ta bayar da cikakkun alkaluman hakan ba.