✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rigakafin COVID-19 na daf da shiga kasuwa

A mako mai zuwa rigakafin cutar Coronavirus za ta shiga kasuwa a Birtaniya yayin da Gwamnatin kasar ta amince a fara amfani da rigakafin ta…

A mako mai zuwa rigakafin cutar Coronavirus za ta shiga kasuwa a Birtaniya yayin da Gwamnatin kasar ta amince a fara amfani da rigakafin ta farko mafi inganci da kamfanonin Pfizer da BioNTech suka samar.

Sakataren Lafiyar kasar Birtaniya, Mista Matt Hancock, ya bayar da tabbacin ingancin rigakafin bisa bayanan da hukumomin da ke kula da ingancin magunguna na kasar suka bayar.

Mista Hancock ya kuma ce a makon gobe allurar riga-kafin cutar dubu 800,000 da suka yi oda za su isa kasar ta Birtaniya.

Birtaniya ita ce kasa ta farko da ta fara amince wa kan fara amfani da rigakafin na COVID-19 a fadin duniya wadda aka samar a kasar Amurka.

A Larabar da ta gabata ne gwamnatin kasar ta amince da maganin da kamfanin hada magunguna na Pfizer-BioNTech ya samar.

Aminiya ta ruwaito cewa allurar mafi inganci da aka samar a duniya, wani likita dan Najeriya Dokta Onyema Ogbagu ya taka rawar gani wajen kirkiro rigakafin cutar COVID-19 din da kamfanin Pfizer na kasar Amurka ya samar.

Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya cikin wata sanarwa da wallafa kan shafinsa na Twitter a ranar Litinin 23, ga watan Nuwamban 2020, ya ce rigakafin shi ne mafi inganci kuma na farko da aka samar a Amurka domin cutar COVID-19.

“‘Yan Najeriya sun ba wa duniya gudunmuwa ta fuskoki da dama kuma muna matukar jinjina ga Dokta Onyema Ogbuagu da ya taimaka aka samar da rigakafin COVID-19”, inji Ofishin.

Pfizer da BioNTech da suka yi rigakafin da Dokta Onyema Ogbuagu ya kirkiro, sun ce shi ne aka fara samarwa na cutar COVID-19, kuma ya warkar da 90% na wadanda aka yi wa amfani da shi.

An yi gwajin allurar rigakafin a kan mutum 43,500 da suka kamu a kasashe shida kuma babu alamar ya haifar musu da barazanar lafiya.

Kamfanin Pfizer ya ce, zai samar da rigakafin guda miliyan 50 kafin karshen 2020, da kuma guda biliyan 1.3 zuwa karshen shekarar 2021.