Rihanna: Shahararriyar mawakiya ta haihu | Aminiya

Rihanna: Shahararriyar mawakiya ta haihu

Rihanna a lokacin da take da juna biyu a Los Angeles, California. – (Hoto: Mike Coppola / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP)
Rihanna a lokacin da take da juna biyu a Los Angeles, California. – (Hoto: Mike Coppola / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP)
    Sagir Kano Saleh

Shahararriyar mawakiyar Amurka kuma mai kamfanin kayan alfarma na Fenty, Rihanna ta haihu bayan juna biyunta da ta yi ta yayatawa.

Kafar TMZ ta ce Rihana da masoyinta A$AP Rocky sun samu da na miiji a haihuwarsu ta farko ne ranar 13 ga watan Mayu, 2022 a birnin Los Angeles na kasar Amurka.

Mujallar People Magazine ta tabbatar da haihuwar, inda ta ruwaita makunsatan mawakan suna cewa, “Rihanna tana cikin koshin lafiya kuma suna farin cikin ganin sun zama mahaifa.”

Sai dai kuma kawo yanzu, Rihanna da A$AP Rocky ba su fito sun sanar da haihuwar ba, ko bayyana suna ko jinsin jaririn nasu.

Hakazalika ba Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya yi kokarin jin ta bakin wakilan mawakan, amma har yanzu ba a same su ba.

A baya-bayan nan ne Rihanna mai shekara 34, haifaffiyar Barbedos ta zama biloniya, inda ta koma harkar kayan kwalliya da tufafin alfarma, lamarin da ya sa ta ja baya da harkar waka.

An jima ana jita-jitar soyayyar Rihanna da A$AP Rocky mai shekara 33 kafin daga baya a 2021 su tabbatar cewa haka abin yake.

A watan Janairu suka sanar cewa mawakiyar na da juna biyu, inda suka fitar da hotonta dauke da juna biyu a Harlem.

Tun daga lokacin hotunanta suka yi ta karade gari, suna nuna yadda cikin nata ke kara girma.

Ita kuma ta sha halartar taruka tana nuna juna biyun nata cikin salo.