✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici ya barke a hedikwatar Jam’iyyar APC

An yi wa Abdullahi Adamu bore a daidai lokacin da ake jiran Tinubu ya bayyana abokin takararsa

Kwamitin Gudanarwar Jam’iyya na tsaka da wani taro a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja ranar Alhamis da dare ne dandazon wasu matasa suka yi dafifi tare da barazana ga Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu.

Hakan kuwa ta faru ne sa’o’i kadan kafin cikar wa’adin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ba wa jam’iyyun siyasa na mika mata sunayen ’yan takararsu na zaben 2023.

Ana zargin matasan da suka yi ta wake-wake suna sukar Sanata Abdullahi Adamu sun fito ne daga Jihar Kogi.

Matasan na zargin cewa uban gidansu ya ci zaben dan takarar Majalisar Wakilai, amma aka ba wa wani daban takara.

Don haka suka yi barazana cewa ba za su bar Abdullahi Adamu ya fita daga sakatariyar jam’iyar ba, lamarin da ya sa jami’an tsaro suka kulle kofar shiga harabar sakatariyar.

Jami’an tsaron sun kuna fitar da ’yan jarida daga harabar, amma daga baya suka sake tantance su saboda dalilan tsaro kafin su bari su koma ciki

Ofishin yakin neman zaben Buhari ya koma hannun Tinubu

A halin da ake ciki dai Ofishin Yakin Neman Zaben Shugaba Buhari na 2019 ya koma na yakin neman zaben Tinubu a 2023.

An damka wa Tinubu ofishin da ke Yankin Kasuwanci na birnin Abuja ne kwanaki kadan bayan ya lashe zaben dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC.

Daraktan Yada Labarai na Kungiyar Yankin Neman Zaben Tinubu a 2023, Bayo Onanuga, ya ce shi ma Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ya zo na hudu a zaben dan takarar ya ba wa Tinubu gudunmawar ofishinsa na yakin neman zabe.

Onanuga ya bayyana cewa ofishin yakin neman zaben Buhari da aka damka wa Tinubu na da kayan sadarwa da tattara bayanai na zamani da kuma cibiyar kiran kar-ta-kwana da sauran kayan aikin ofis.