✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici ya barke a taron shugabannin PDP na Arewa

Tun kafin a fara ’yan daba suka mamaye wurin, suka kwace tare da lalata kayan zabe

Riciki ya barke a taron jam’iyyar PDP na yankin Arewa maso Yammacin Najeriya inda aka ba hamata iska tsakanin magoya bayan manyan ’yan takara.

Taron na yankin an gudanar da shi ne domin zabar shugabannin PDP na yankin, wanda manyan ’yan takarar Mataimakin Shugaban jam’iyyar na Yankin Arewa maso Yamma suka hada da Sanata Bello Hayatu Gwarzo, Aminu Wali da kuma dan takarar tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Wasu majiyoyi sun ce an ba hamata iska a wurin taron tsakanin magoya bayan tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Sakkwato, Hon. Aminu Waziri Tambuwal, wanda Kwankwason ke zargi da yin katsalandan a harkokin jam’iyyar a Jihar Kano.

Fada ya kaure a wurin taron ne bayan rashin gamsuwar bangarorin da tsarin zabenda kuma ’yan takarar da aka tsayar, lamarin da ya kai ga farfasa akwatuna da kekketa takardun zaben.

Aminiya ta gano cewa tun kafin a kai ga fara zaben, ’yan daba suka mamaye wurin taron, suka kwace tare da lalata kayan zaben, yayin da mutane suka ce kafa me na ci ban ba ki ba.