✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici ya barke tsakanin APC da PDP kan biliyoyin Daloli

APC ta nemi PDP ta yi bayanin Dala biliyan 16 na gyaran wutar lantarki; PDP ta ce APC ta yi bayanin Naira biliyan 800 da…

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta kalubalanci jam’iyyar hamayya ta PDP da dan takararta na shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, da su yi bayanin kwangilar Dala miliyan 460 da gwamnatin PDP ta bayar domin sanya kyamarorin nadar bayanai ta bidiyo a shekarar 2010 ba tare da an yi aikin ba.

APC ta ce tana kuma neman cikakken bayani kan rancen Dala biliyan biyu da gwamnatin PDP ta karba daga kasar China daga shekarar 2010 zuwa 2013.

Sai dai a martanin da PDP ta bayar ta ce neman “shashantar da zargin da ake wa APC na neman jinginar da Najeriya”, ya tabbatar cewa akwai kanshin gaskiya a zargin da ake wa APC.

Mahawarar ta fara ne bayan Atiku da PDP a lokuta daban-daban a ranar Lahadi sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi gafarar ‘yan Najeriya kan “rancen kasashen waje da yake karbowa ba tare da yin wani abin a zo a gani ba”.

Amma Mataimakin Sakataren Yada Labaran APC na Kasa, Yekini Nabena, a sanarwar da ya fitar ya kalubalanci PDP ta bayyana yadda aka yi ta kashe Dala biliyan 16 na samar da wutar lantarki “ba tare da samar da wutar ba”.

Ya kuma bukaci PDP da ta yi bayanin “badakalar tallafin man fetur da kudin yaki da ‘yan ta’adda da aka karkatar aka raba wa mukarraban siyasar”, gwamnatin PDP da dai sauransu.

“Ku tuna cewa aikin da ya susuce, Marigayi Shugaba Umaru Yar’Adua ne ya kirkire shi sannan tsohon Shugaba Jonathan ya bayar da kwangilar a 2010 domin taimaka wa hukumomin tsaro a Birnin Tarayya wajen magance matsalolin tsaro.

“Tun da aka kulla yarjejeniyar Najeriya ke ta biyan China, amma ‘yan Najeriya ba su ga kaymarorin ba, kuma babu wani bayani game da aikin. Ya kamata bangaren majalisa ya binciki lamarin”, inji APC.

Amma Sakataren Yada Labaranta na Kasa, Kola Ologbondiyan a martaninsa ya ce, “Martanin APC game da yunkurinta na jefa ‘yan Najeriya da za a haifa nan gaba cikin bauta a hannun China, ya nuna APC ba mutane APC ta sa a gaba ba kuma ba ta nadamar kurakuran shugabanninta da kuma gwamnatinta”.

“Jam’iyyarmu na so APC ta fara yin bayani a kan Naira biliyan 800 da ta ce ta kwato tukuna, saboda ‘yan Najeriya sun riga sun gano cewa APC na samun karuwa da damfara da kuma rashawa”, inji sanarwar.