✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici ya barke tsakanin Matafiya da Ma’aikatan Jirgin sama a Kano

Matafiyan da ma'aikatan sun shiga ba wa hammata iska, yayin aka fasa bakin wani matafiyi.

Rikici ya barke tsakanin matafiya da ma’aikatan kamfanin jiragen sama na Azman a Kano, bayan an samu tsaikon tashin wani jirgin fasinja.

Tun farko jirgin an sanar da cewa zai tashi da misalin karfe 7:30 na safe, sai aka sake maida shi 8:30 na dare a ranar Juma’a, lamarin da ya janyo zanga-zanga a filin jirgin saman na Malam Aminu Kano.

Sai dai zanga-zangar ta rikide ta koma rikici a tsakanin matafiya da ma’aikatan Azman da kuma ma’aikatan filin tashin jiragen.

Aminiya ta samu cewa rikicin ya kai ga wata ma’aikaciya ta yanke jiki ta fadi sannan an fasa wa wani fasinja baki yayin da kuma aka kusa yi wa wani ma’aikacin jirgin saman tsirara saboda irin yadda aka keta masa suturar da ke jikinsa.

Irin haka ta faru a daren ranar Alhamis, yayin da jirgin Azman ya fasa tasowa daga Abuja zuwa Kano saboda samun matsala da ya yi.

Daga bisani aka sake sauya wa matafiyan lokacin tashi zuwa karfe 4:30 na yammacin ranar juma’a.

Sai dai fasinjojin sun fusata saboda rashin bayyana musu dalilin sauye-sauyen lokacin tashin nasu.

Kuma babu wani ma’aikaci daga kamfanin jirage na Azman da ya yi wa fasinjojin jawabin dalilin aikata hakan.

Wasu daga cikin fasinjojin sun koka kan yadda ba a sama musu masauki ba balle kudin abun hawa.