✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikici ya barke yayin gangamin APC a Kano

Lamarin dai ya kusa ya tarwatsa taron gaba daya kafin daga bisani a shawo kansa.

Wani rikici ya barke yayin babban gangamin jam’iyya mai mulki ta APC a jihar Kano a ranar Asabar.

Gangamin, wanda aka shirya shi domin bikin karbar tsohon dan takarar Gwamnan Jihar a karkashin jam’iyyar GPN a zaben shekarar 2019, A. A. Zaura da ma wasu wadanda suka yi kaura zuwa jam’iyyar, ya gudana ne a unguwar Sabon Gari da ke cikin birnin na Kano.

Rahotanni sun ce rikicin ya fara ne a daidai lokacin da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Hamisu Ibrahim Chidari ke gabatar da jawabi, a inda wasu ’yan jam’iyyar suka fara ba hammata iska.

Lamarin dai ya kusa ya tarwatsa taron gaba daya bayan da mutane suka fara ranta a na kare domin tsira da rayuwarsu.

To sai dai daga bisani an sami nasarar kwantar da tarzoma kuma al’amura sun ci gaba kamar yadda aka tsara.

APC dai ta ce wasu daga cikin wadanda take bikin karbar sun sauya sheka ne daga jam’iyyar adawa ta PDP tsagin Kwankwasiyya wacce tsohon Gwamnan Jihar, Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi wa jagoranci.

Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje dai na daga cikin manyan bakin da suka halarci taron.

Ko a ranar Alhamis dai sai da Gwamna Ganduje ya yi barazanar sa kafar wando daya da duk wanda ya yi yunkurin tayar da zaune tsaye yayin taron, ko da kuwa wanne dan takara ne ya tsaya masa.