✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Rikici ya hana yara miliyan 222 zuwa makaranta a duniya’

“Kazalika, yara miliyan 120 da ke zuwa makarantar ba sa iya karatu da lissafi."

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla kananan yara miliyan 222 ne rikice-rikice suka hana zuwa makaranta a fadin duniya.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wani rahoto da majalisar ta fitar ranar Talata.

Daraktar Ilimi ta majalisar, Yasmine Sherif, ta ce amma idan aka fitar da kudade, za a iya tallafa wa yaran cikin gaggawa.

“Mun gano akalla yara miliyan 222 da ya kamata su rika zuwa makaranta amma rikici ya hana su zuwa a fadin duniya,” inji Majalisar.

Rahoton ya kuma ce kusan yara miliyan 78 ’yan tsakanin shekara uku zuwa 18 ne ba sa samun ilimi kwata-kwata.

Majalisar ta kuma ce akwai wasu yaran su miliyan 20 da suke zuwa makarantar, amma sam ba sa samun shawarwarin da ya kamata su rika samu yayin karatun nasu.

“Kazalika, yara miliyan 120 da ke zuwa makarantar ba su iya karatu da lissafi ba.

“Fiye da rabin makarantun da ke kasashe matalauta kuma ba su da hanyoyin samar da ruwa tsaftatacce a cikinsu, kuma kaso 40 cikin 100 na yaran ne kacal ke iya wanke hannuwansu.

“Kaso daya bisa uku na wadannan makarantun ne kawai suke da isasshiyar wutar lantarki a makarantunsu.”

Kwamitin Majalisar ya kuma ce yana aiki a kasashe irin su Afghanistan da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da Sudan ta Kudu da kuma Yemen, sannan yana tallafa wa yara da ’yan gudun hijira a Ukraine. (NAN)