✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin Ali da Zango: Asalinsa da yadda karamar magana ta zama babba

A yanzu dai za a iya cewa ginin dangantaka na shekara 18 a tsakanin fitattun jaruman fina-finan Hausa, Ali Nuhu da Adam A. Zango ya ruguje…

A yanzu dai za a iya cewa ginin dangantaka na shekara 18 a tsakanin fitattun jaruman fina-finan Hausa, Ali Nuhu da Adam A. Zango ya ruguje bayan Ali ya kai Zango gaban kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge a Kano bisa zargin bata masa suna da cin mutunci.

Wannan matakin bai zo da mamaki ga masu bibiyar masana’antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood ba, kasancewar dangantaka a tsakanin jaruman ta dade da yin tsami, musamman yadda suka rika samun sabani tun wasu shekaru da suka gabata.

Sai dai a yanzu an sake kafa tubulin ginin sabuwar dangantaka tsakanin jaruman, kasancewar  kafin a kai ga shiga kotu, Kwamitin Sasantawa na Kungiyar ’yan fim ta Motion Pictures Practitioners Association (MOPPAN) ya sasanta jaruman a Kano a ranar Asabar da ta gabata.

Alhaji Salisu Mu’azu Jos ne ya jagoranci kwamitin sasantawar, sauran ’yan kwamitin sun hada da Shugaban Kwamitin Amintattu na Kungiyar MOPPAN, Abdulkareem Mohammed da Shugaban MOPPAN na Kasa, Abdullahi Maikano da kuma wadansu daga Arewa Filmmakers Association of Nigeria, AFMAN, kamar Baba Karami da Sani Real Lobe da sauransu.

Idan ba a manta ba wutar rikici a tsakanin jaruman ta dade da kamawa amma ba ta famtsama kamar wutar daji ba sai a watan Fabrairun shekarar 2014 lokacin jaruman sun cika shekara 14 da haduwa a Kannywood.

A shekarar 2014 ne Zango ya bayyana wa duniya cewa ya yanke alakar da ke tsakaninsa da Ali Nuhu cikin wata hira da ya yi da Aminiya.

Ya ce ba zai yarda ya ci gaba da alaka da maigidansa ba, saboda ba zai yarda da tafiyar da babu gaskiya a cikinta ba.

Wutar rikicin ta 2014 a tsakanin jaruman da ta fi bayyana a duniya ta barke ne bayan jaruma Rahama Sadau ta shiga turakarta ta Instagram ta gasa wa Zango bakaken maganganu saboda ya cire ta a fim dinsa mai suna ‘Duniya Makaranta.’

Duk da cewa daga baya jarumar ta ba jarumin hakuri, amma wutar rikicin ta ci gaba da ruruwa, kasancewar dan gani kashe nin Zango a lokacin mai suna Ali Artwork ya rama wa ubangidansa zagin da aka yi masa, inda ya yi wa Ali Nuhu tatas.

Hakan ya sanya yaran Ali Nuhu a lokacin wadanda suka hada da Garzali Miko da Shamsu Dan’iya da sauransu suka kai karar Ali Artwork, aka hada su da ’yan sanda don a kama Ali Artwork, amma ba su same shi ba, a nan aka kama mahaifinsa. Daga baya ya kai kansa bayan mahaifiyarsa ta yi barazanar tsine masa.

A lokacin Zango ya ce:  “Yau rana ce da zan fadi abin da al’umma ba su sani ba, domin suna yi mini kallon ni yaron Ali Nuhu ne. Wannan kalma mai suna yaro a wurin Ali ni ne na dauka na dora masa, na kuma ce shi ubangidana ne. A shekara 14 da nake fim a industiri, sunana ya yadu a duniya, ni nake yi wa Yakubu Muhammad da Abubakar Sani da Sadi Sidi Sharifai da Mudassir Kassim da Adam Kirfi da Adamu Nagudu da sauransu kida. Sunana ya shiga duniya.”

Ya ce ya bukaci furodusoshi su sanya shi a fim amma suka ki, har sai da ya tara kudi ya yi wa kansa fim mai suna ‘Surfani’, daga nan furodusoshi irin su Bauni da Ali Nuhu da Najjashi SB Jakara suka fahimci yana da hazaka za su iya sa shi a fina-finansu.

“A wannan lokaci ne Najjashi ya yi mini fim mai suna ‘Misali,’ Bauni ya yi mini ‘Dukiya’, Ali Nuhu kuma ya yi mini ‘Zabari’, saboda haka a wancan lokacin sai na dauki wadannan mutane a matsayin iyayen gidana,

“Amma sai na fifita Ali a kansu, saboda a wancan lokacin shi ne ya yi mini fim din da na fi suna. Wannan dalilin ya sa na dauki suna na ba shi na matsayin mai gidana, ba wai don wani abu ba. Don haka ina so duniya ta sani cewa ni na yi wa kaina komai a masana’antar fim kafin wani ya taimake ni,” inji Zango.

Zango ya sha zargin cewa Ali Nuhu yana sa yaransa su zage shi, kuma ya sha kai kararsu wurin Ali amma ba ya hana su ko daukar mataki a kansu.

Wannan takaddamar ta shafe wata biyar ana yin ta, inda a watan Yuli, 2014 aka sasanta jaruman bayan da aka yi zaman sulhu a otel din Gamji da ke Kaduna,

An yi sasanci ne a karkashin kwamitin sulhu, wanda Shugaban Kungiyar MOPPAN a lokacin, Malam Khalid Musa ya jagoranta.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da Darakta kuma Furodusa Abu Sarki da Furodusa Tahir I. Tahir da Furodusa Abdul Amart da Darakta Sadik N. Mafiya da kuma mai daukar hoto Isma’il M. Isma’il.

A lokacin zaman jaruman sun gabatar da jawabai masu daukar hankali, inda suka bayyana sabanin a matsayin aikin Shaidan, sannan suka bayyana farin cikinsu ganin wannan rana da komai ya koma daidai.

A yayin zaman an kuma shirya abubuwan da suka shafi zumunci, inda za a yi taron shan ruwa a gidan Ali da kuma Zango, sannan kamfanonin jaruman biyu suka amince za su shirya wa juna fim.

Wata majiya da ta halarci sulhun ta bayyana wa Aminiya cewa: “Akwai fim yanzu na kamfanin Ali Nuhu wato FKD Production, Adamu ne babban jarumi, shi kuma Ali Nuhu zai tallafa masa, haka kuma shi ma kamfanin Prince Zango na Adam A. Zango ya shirya wa Ali Nuhu fim, inda kuma Adamu zai tallafa masa.”

A lokacin ne Furodusa Abdul Amart ya shirya wa jaruman fim mai suna ‘Akasi’ a karkashin kamfanin Abnur Entertainment. Abdul Amart don a nuna wa duniya komai ya wuce a wurin jaruman.

Rikici tsakanin jaruman da ya sake kamari na tsawon shekara daya da watanni wato daga Janairu 2017 zuwa Fabrairu 2018 ya faru ne lokacin da jarumi Ali Nuhu ya nuna fim dinsa mai suna ‘Mansoor’ a wata silima da ke Shoprite a birnin Kano, inda Zango bai je ya kalli fim din ba, wannan ta sanya yaran Ali Nuhu suka fara guna-guni, na Zango ma suka fara mayar da martani.

Aminiya ta gano hatsaniyar ta kara habaka ne bayan Ali Nuhu ya ki zuwa kallon fim din ‘Gwaska Returns’ na jarumi Zango, wanda aka nuna a silima a Kano, inda a nan ma yaran Zango suka ci gaba da guna-guni.

Hatsaniyar ta lokacin ta dauki sabon salo ne lokacin da ake daukar fim din darakta Kamal S. Alkali, inda Zango ya zo wurin daukar fim din, sai aka samu Ali Nuhu ba ya da lafiya, inda yake kwance a wani daki.

Wata majiya ta fada wa Aminiya cewa “Bayan an sanar da Zango cewa Ali Nuhu na kwance ba ya da lafiya a wani daki ne, sai ya ce ba zai je ya gaishe shi ba, al’amarin da ya sanya magoya bayan jaruman suka fara yakin cacar-baki a shafin Instagram.”

Al’amarin da ana cikin haka sai Adam A. Zango ya sanya hotonsa hade da wasu kalamai da yaran Ali Nuhu suka zarga cewa da ubangidansu yake, su ma suka mayar da martani.

Wannan takaddama dai shahararren darakta Falalu Dorayi da furodusa Sani Sule ne suka jagoranci sasantarwa, inda a karshe kwalliya ta biya kudin sabulu.

A lokacin jaruman sun sasanta, sun rungumi juna, sun yafe wa juna, inda suka dauki hotuna daban-daban.

Wannan rikicin na yanzu da ya barke har ta kai ga Ali Nuhu ya kai Zango kotu kuwa ya fara ne tun a watan Oktoban bara, lokacin da aka ba Ali Nuhu lambar girmamawa ta Dokta a kasar Togo, inda ’yan fim suka rika taya Ali Nuhu murna a shafin Instagram amma Zango bai taya shi ba.

Wata majiya ta bayyana wa Aminiya cewa hakan ya sa yaran Ali Nuhu suka fara guna-guni a kan batun.

“Rashin taya Ali Nuhu murna ya sa dangantakarsu ta fara rawa, ana cikin hakan sai Ali Nuhu ya yi bikin cika shekara 20 a Kannywood, ya yi bikin cika shekara 45 da haihuwa, ya yi bikin cika shekara 16 da aure, duka Zango bai taya shi murna a Instagram ko Facebook ko ya kira shi a waya ko tura masa sako ba. Wannan bai yi wa Ali Nuhu dadi ba, amma bai ce komai ba saboda zurfin ciki,” inji wata majiya.

Ana cikin haka ne sai Zango ya dora wani bidiyo a shafinsa na Instagram inda furodusa Kawu Kamfa da Aminu Mugu suke rika zage-zage.

Zango ya yi zargin cewa Ali Nuhu ne ya sa su zage shi, duk da cewa a bidiyon ba su kama sunan Zango ba.

Daga nan bayan kwana biyu sai Zango ya fitar da wata sanarwa a shafin Instagram, inda ya zagi jarumi Ali Nuhu, hakan ne ta sa Ali ya ce an zo wurin, inda bayan wasu kwanaki sai ga takardar sammaci daga Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge, inda Ali Nuhu ya yi karar Zango bayan ya zarge shi da bata masa suna hade da cin mutuncinsa.

A yayin da yake yi wa Aminiya bayani bayan an kammala zaman sasantawar, Shugaban Kwamitin, Salisu Mu’azu Jos ya ce zaman ya haifar da da mai ido tunda ya yi nasarar sasanta jaruman.

Ya ce, “Mun yi zama, zaman kuma ya samar da abin da ake bukata, saboda mun saurari kowa a cikinsu, sun kuma amayar da abin da ke cikinsu gaba daya, abin da muka fahimta shi ne, matsalar ba wai tsakaninsu ba ce saboda kowannensu, ya fadi iya yadda yake girmama kowa. Amma yaran da ke tsakaninsu ke haddasa fitintinu. Shi Adamu ya tabbatar da cewa ya yi wa Ali ba daidai ba, saboda ya kai ga ya yi zagi, a wannan wurin ya ba Ali hakuri, ya roki Ali ya yafe masa, inda Ali Ya yafe masa. Sannan Ali ya bayyana mana cewa zai janye batun karar da ya shigar kotu.”

Ya ce dukkan jaruman sun bayyana cewa za su yi bakin kokarinsu don ganin hakan bai sake faruwa ba, “Tabbas sun fadi haka, sannan muka ce su je su yi wa magoya bayansu fada, sannan mun dauki hukunci cewa daga yau din nan duk wani dan fim da ya shiga kafar sadarwa sannan ya yi batanci ga wani, to za a yanke masa hukunci daidai da laifinsa,” inji shi.

Abin jira a gani shi ne ko wannan sasanci zai dore, bisa la’akari da cewa ba wannan ne lokaci na farko da ake sasanta jaruman bayan sun samu sabani ba.