✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Amurka: Za a fara kada kuri’ar tsige Trump

kaso 55 na ‘yan kasar, ciki har da wasu jiga-jigan jam’iyyar Republican na son ganin an tsige Trump.

Majalisar Dokokin Amurka ta fara shirin kada kuri’a a karo na biyu don tsige Shugaba Donald Trump mai barin gado, a ranar Laraba.

Wannan shi ne karo na biyu da Majalisar ta yi kokarin tsige Trump din cikin watanni 13 da suka gabata.

Sai dai mataimakinsa, Mike Pence, a ranar Talata ya bukaci da a yi watsi da kiraye-kirayen da ake na amfani da kundin tsarin mulkin kasar wajen tsige Mista Trump.

Mike Pence ya yi watsi da bukatar da Shugabar Majalisar, Nancy Pelosi ta aike masa, na ganin ya yi amfani da sashe na 25 na kundin tsarin mulkin kasar, wajen tsige Trump.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da sakamakon kuri’ar ra’ayi da aka kada, ya nuna kaso 55 na ’yan kasar, ciki har da jam’iyyar Republican da Liz Cheney na goyon bayan a tsige Mista Trump.

Sai dai Trump ya musanta zargin da ake cewa, shi ne ya aike da bata-gari zuwa Ginin Capitol wanda ke dauke da Majalisun Kasar.

A satin da ya gabata ne, kafofin sadarwa na Facebook, Instagram, Twitter suka dakatar da Trump daga amfani da su har zuwa bayan mulkinsa, saboda gudun tada tarzoma.

A ranar Laraba ma kafar Yotube, ta dakatar da Mista Trump daga amfani da kafar.

Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta ‘Human Rights Watch’ ta roki Shugaban Amurka mai jiran gado, Joe Biden da ya ladabtar da Trump kan abin da ya aikata, da zarar an rantsar da shi a ranar 20 ga Janairu, 2020.

Human Right Watch ta ce dole ne Trump, ya fuskanci  hukunci kan laifukan da ya aikata da suka shafi take hakkin dan Adam, haddasa rikici da kuma tunzura jama’a.