✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin APC a Kano: Ganduje da Shekarau sun sa labule da Buni

A karon farko Ganduje ya halarci zaman sulhu tsakanin bangarensa da na Malam Ibrahim Shekarau.

A karon farko, Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya halarci zaman sulhun da uwar jam’iyyar APC ke yi tsakanin bangarensa da na tsohon gwamnan jihar, Sanata Malam Ibrahim Shekarau.

Ganduje da Shekarau da suka kasance ba sa ga-maciji da juna sun yi ganawar sirri da Shugaban Riko na Jam’iyyar APC na Kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ranar Juma’a a Abuja, kan rikicin shugabancin da ya dabaibaye jam’iyyar a Jihar Kano.

Daraktan Yada Labaran Buni, Mamman Mohammed, ya tabbatar wa Aminiya da dare cewa: “Ganduje da Shekarau sun nuna kwarin gwiwarsu cewa nan ba da jimawa ba za a sasanta rikicin.” 

Karon farko ke nan da Ganduje ya halarci taron da kansa, tun bayan da Buni ya fara jagornatar ganawa da bangarorin da ke rikicin domin sasanta su.

Mamman Mohammed ya ce Sanata Barau Jibril daga bangaren Shekarau ma ya halarci zaman.

Takun sakar da ke tsakanin bangarorin biyu dai ya samo asali ne daga rikicin shugabancin Jam’iyyar APC a Jihar Kano.

Bangaren Ganduje na daukar Abdullahi Abbas a matsayin Shugaban Jam’iyya, a yayin da bangaren Sanata Shekarau ke daukar Ahmadu Haruna Zago (Dan Zago) a matsayin Shugaban Jam’iyya.

Rikicin dai ya ki ci, ya ki cinyewa, har ta kai su ga kotu, inda aka yi ta tabbatar da Danzago da shugabannin da ke bangaren Shekarau a matsayin halastattu.

Sai dai kuma sun fito ne daga bangaren Shekarau, wanda ke zaman doya da manja da Gwamna Ganduje, wanda a halin yanzu shi ne Jagoran APC a jihar.

A kan haka ne uwar jam’iyyar ta kafa kwamitin sasanta bangarorin, wanda ya kai ga ganawar sirrin ta ranar Juma’a.

Kwamitin dai ya kasance ne a karkashin jagorancin Mai Mala Buni da Gwamnan Jihar Jigawa Badaru Abubakar da tsohon Shugaban Majlaisar Wakilai Yakubu Dogara.

A lokacin zamansu na farko a makon jiya, Sanata Kabiru Gaya ne ya wakilci bangaren Gwamna Ganduje, shi kuma Sanata Ibrahim Shekarau ya wakilci bangarensa.

Majiyar Aminiya ta ce a lokacin zaman na farko, bayan jawaban da aka gabatar na neman daidaitawa tare da alkawarin yin adalci ga kowa, dukkan bangarorin biyu sun amshi tayin uwar jam’iyyar na ajiye makamansu su dunkule a wuri guda.

Majiyar ta kara da cewa sai dai akwai batutuwan da suke da sarkakiya wadanda suka sa ba a iya kare sulhun a lokaci guda ba.

Misali dambarwar shugabancin jam’iyyar wanda yanzu haka yake gaban kotu da kuma jerin bukatun da kowane banagre ke rokon ganin ya rabauta da su a zaman sulhun.