✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin APC a Kano: Tsohon Mataimakin Ganduje ya koma tsagin Shekarau

Farfesa Hafiz Abubakar ya ce bangaren Sanata Ibrahim Shekarau ne dahir.

Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Farfesa Hafiz Abubakar, ya saki bangaren Gwamna Abdullahi Ganduje ya kama na Sanata Ibrahim Shekarau inda ya kafa shekarsa ta ci gaba da tafiyar da harkokin siyasa.

A wata hira da ya yi da manema labarai ranar Talata a gidan Shekarau, Farfesa Hafizu ya ce ya koma tsagin Sanata Shekarau wanda ya bayyana a matsayin bagaren da zai tabbatar da kyakkyawar makoma a jam’iyyar.

“Na dawo bangaren Shekarau wanda shi ne tsagin da yake tabbatar da kwararar romon dimokuradiyya kuma yake tafiya da kowa a tsarin gudanarwarsa.

“Ina da yakinin cewa tsarin jagoranci da Sanata Shekarau ya dauko shi ne zai kai jam’iyyar APC a Jihar Kano zuwa ga ci.

“Saboda haka ina ganin ya kamata mu hada kai a yi tafiyar nan da mu domin mutunta juna da bai wa ra’ayin al’umma muhimmanci,” a cewar Farfesa Hafiz.

Tsohon Mataimakin Gwamnan ya ce rikicin siyasa da ya dabaibaye jami’yyarsu ta APC na daya daga cikin abubuwan da suka sanya ya yanke shawarar koma wa tsagin Sanata Shekarau.

Ana iya tuna cewa, a bayan nan ne rikicin siyasa da ya tsananta a jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ya sanya bangaren Gwamna Ganduje ya zabi Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar na Jihar yayin da kuma tsagin Sanata Shekarau ya zabi Ahmadu Haruna Danzago a matsayin shugaban jam’iyyar inda kowane bangare ya gudanar da zaben shugabannin jam’iyyar daban-daban a lokaci guda.

A kan haka ne Farfesa Hafizu ya bayyana takaicinsa da cewa, rikicin ya saba da manufar jam’iyyar kuma hakan zai kai ga fuskantar matsala a zaben 2023.

Farfesa Hafiz ya ce bangaren Gwamna Ganduje ba ya tafiya da ’yan jam’iyya domin kuwa “duk lokacin da wani abu ya faru cewa suke yi “‘jam’iyyar APC ta mutum uku ce: Gwamna da Matarsa da Shugaban jam’iyya’”.

Farfesa Hafiz wanda a shekarar 2018 ya yi murabus daga kujerar Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, ya sake koma wa bangaren Gwamna Ganduje a 2019.

Ya yi wa Ganduje mataimaki daga shekarar 2015 zuwa 2018 domin tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar karkashin inuwar jam’iyyar PDP a zaben 2019.

Sai dai takaici ya sanya Farfesa Hafiz ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa PRP bayan da jam’iyyar PDP ta tsayar da Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takararta, kuma ya rasa tikitin tsayawa takara a jam’iyyar PRP da ya koma.

Hakan ne ya sanya bayan zaben 2019 ya sake komawa tsagin Gwamna Ganduje a jam’iyyar APC.