✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta soke zaben Sanata Bwacha dan takarar Gwamnan Taraba a APC

Kotu ta umarci INEC ta kwace takardar shaidar cin zaben da ta bai wa Bwacha a gudanar da sabon zabe cikin kawan 14

Babbar Kotun Tarayya ta soke zaben Sanata Emmanuel Bwacha a matsayin dan takarar Gwamna na Jam’iyyar APC a Jihar Taraba.

Bayan soke zaben dan takarar gwamna da Sanata Bwacha ya lashe, alkalin kotun, Mai Sharia Simeon Amobeda, ya ba da umarnin gudanar da sabo a cikin kwana 14 .

Kotun ta soke zaben dan takarar ne bayan Cif David Kente da ya yi zawarcin tikitin, ya garazaya gabanta yana neman ta ba da umarnin sakewa.

Mai Shari’a Amobeda ya ce wanda aka yi kara ya kasa gamsar da kotun cewa jam’iyyar ta gudanar da zaben dan takarar gwamna da yake ikirarin cewa ya lashe.

Ya kuma umarci Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta soka takardar shaidar lashen zaben dan takarar gwamna da ta bai wa Sanata Bwacha.

Da yake mayar da martani, lauyan Sanata Bwacha, Ibrahim Effiong, ya ce za su yi nazari kan hukuncin kotun domin yanke shawara kan mataki na gaba da za su dauka.

A nasa bangaren, lauyan jam’iyyar APC, Festus Idepefo, SAN, ya ce za su tattauna da jam’iyyar kan abu na gaba da ya kamata su yi.

Amma, Kente ya yaba wa hukuncin da kotun ta yanke, yana mai cewa lokacin yin kama-karya ya zama tarihi.

Ya bayyana cewa kwararan hujjojin da aka gabatar wa kotun ne suka gamsar da ita kamar yadda ‘yan jam’iyyar suka sani cewa ba a gudanar da zaben dan takarar gwamna a jam’iyyar APC ba.