✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin APC: Mataimakan Abdullahi Adamu sun bukaci NWC ta juya mishi baya

Mambobin Kwamitin Gudanarwar Jam'iyyar APC na Kasa sun yi fito-na-fito da Abdullahi Adamu

Sabon rikici ya kunno kai a Hedikwatar Jam’iyyar APC na Kasa, inda Mataimakan Shugaban Jam’iyyar na Kasa suka bukaci mambobin Kwamitin Gudanar Jam’iyyar (NWC) da su yaki abini da suka kira kama -karyan da Shugaban Jam’iyyar na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, yake yi.

Sabon rikicin ya taso ne bayan Mataimakan Shugaban Jam’iyyar na Kasa daga yankin Arewa maso Yamma, Salihu Mohammed Lukman da takwaransa na yankin Kudu maso Yamma, Asaac Kekemeke, sun zargi Abdullahi Adamu da fakewa da sunan Shugaba Buhari, wajen yin gaban kansa a harkokin jam’iyyar.

“Yana yin gaban kasa ta hanyar yi wa mambobin NWC amfani da sunan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, domin su amince da abin da yake so;

“Duk kokarin da aka yi domin ganin shugaban jam’iyyar ya mutunta doka da kuma hurumin NWC da aka zaba a ranar 26 ga watan Maris a Babban Taron Jam’iyyarmu, abin ya ci tura.

“To ku tuna cewa Kwamitin Zartarwar Jam’iyya (NEC) ya mika ikonsa ne ga NWC ba wai ga Shugaban Jam’iyya ko wani mahaluki ba.”

Don haka suka bukaci sauran mambobin Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar da su hada kai su yaki Abdullahi Adamu.

Wannan sabon rikicin ya taso ne bayan mako biyu ana dage zaman kwamitin gudanarwar jam’iyyar ba tare da wani dalili ba, a daidai lokacin da harkokin siyaya ke kaiwa kololuwarsu.

Sanarar hadin gwiwa mataimakan shugaban jam’iyyar suka fitar kan zargin Abdullahi ta ce, “A matsayinmu na mambobin NWC kuma mutanen da mambobin jam’iyya suka ba mu hurumi, muna sanar da Mai Girma Abdullahi Adamu, da kuma sauran shugabannin APC cewa;

“Daga yanzu, duk wani umarni da Shugaban Jam’iyya na Kasa ko wani jami’in jam’iyya ya bayar ba tare da sahalewar NWC ba, kamar yadda kundin tsarin jam’iyya ya tanada, to haramtacce ne kuma shiga hurumin NWC ne; sai dai idan NWC ko wani halastaccen bangaren jam’iyyar ne ya tabbtar da shi.

“Babu wani mamban NWC da aka zaba a Babban Taron Jam’iyya APC na ranar 26 ga watan Maris, 2022 domin ya dumama kujera ko ya zama dan kallo a hedikwatar jam’iyya.

“Saboda haka, ya kamata sauran mambobin NWC su zo mu hada kai mu yaki wannan kama-karya don mu ceto jam’iyyarmu tare da mayar da ita a bisa turbar da aka kafa ta na ciyar da Najeriya gaba a bisa gaskiya da adalici da rikon amana da kuma rashin son zuciya wajen gina jam’iyyar. Allah Ya albarkci APC!

“A tsawon wata biyu da shugabancin jam’iyyar da kuma NWC ya koma hannun Sanata Abdullahi Adamu domin gudanar da harkokin jam’iyya na yau da kullum, har yanzu babu abin da ta yi, sai dumama kujera; hatta umarnin NEC wanda Sashe na 13.4 na Kundin Tsarin Jam’iyyar APC ya tanada ba a aiwatar ba.

“A matsayinmu na jam’iyya mun ga abin kunya iri-iri a gaban kotu kan saba kundin tsarin jamiyya daga bangaren shugabannin jam’iyyar.

“Dole ta sa muka fitar da wannan sanarwa saboda yadda aka yi ta dage zaman NWC sau biyu a cikin sa’a 48.