✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin APC: Sabuwar takaddama tana ruruwa a Jihar Zamfara

Muddin babu hadin kai jam’iyyar za ta iya gamuwa da matsala.

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Abdul’aziz Yari ya yi watsi da sabon kwamitin rikon kwarya na mutum uku da aka kafa don tafiyar da lamuran Jam’iyyar APC a jihar.

Uwar jam’iyyar ta kasa ce ta kafa kwamitin domin daidaita al’amura a jihar, sakamakon barakar da ta kunno a cikinta sanadiyyar komawar Gwamnan Jihar, Alhaji Bello Matawalle Jam’iyyar APC daga PDP.

Alhaji Abdul’aziz Yari, wanda a baya shi ne jagoran jam’iyyar a jihar kafin raba shi da mukamin, bayan sauya shekar Gwamna Bello Matawalle, ya soki Shugaban Riko na Jam’iyyar ta Kasa kuma Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni kan kaddamar da kwamitin.

Ya shaida wa BBC cewa rusa shugabannin jam’iyyar da maye gurbinsa da kwamitin rikon kwarya saboda shigowar Gwamna Matawalle cikin APC “Babban kuskure ne wanda hankali ba zai dauka ba.’’

Zan iya kai kara kotu kan rashin bin ka’ida

Alhaji Abdul’aziz Yari ya ce Shugaban Rikon Jam’iyyar ta Kasa, Alhaji Mai Mala Buni ba ya da ikon sauya shugabannin jam’iyyar, kuma hakan da aka yi ka iya “tayar da zaune-tsaye.’’

Ya kara da cewa wadanda aka nada a kwamitin rikon jam’iyyar a jihar ba ’ya’yan Jam’iyyar APC ba ne, inda ya yi zargin cewa, “dukkansu babu mai katin Jam’iyyar APC ko daya,’’inji shi.

Tsohon Gwamnan ya ce muddin ’ya’yan jam’iyyar ba su hada kansu ba, to jam’iyyar za ta iya gamuwa da matsala.

Don haka ya bukaci a mai da hankali wajen kawo gyara a jam’iyyar kuma kada a yi abin da zai iya “rusa jam’iyyar.’’

Daya daga cikin aikin kwamitin dai shi ne sabunta rajistar ’ya’yan jam’iyyar a jihar, abin da yake nufin hatta tsofaffin ’ya’yan jam’iyyar za su sake yin rajista.

To amma tsohon Gwamnan ya ce soke sahihancin rajistar ’ya’yan jam’iyyar da ake da ita da kuma yunkurin sabunta rajistar, da cewa ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar kuma zai iya zuwa kotu domin kalubalantar haka.

Martanin Shugaban Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara

Sai dai Shugaban Kwamitin Rikon Jam’iyyar APC a jihar, wanda aka dora wa alhakin sasanta rikicin siyasar jihar da kuma sabunta rajistar ’ya’yan jam’iyyar, Sanata Hassan Nasiha, ya musanta zarge-zargen rashin bin ka’ida.

Alhaji Hassan Nasiha ya shaida wa BBC cewa muddin Alhaji Abdul’aziz Yari bai yarda da shugabancin kwamitin ba, to “Bai yarda da shugabancin jam’iyyar na kasa ba ke nan.’’

Dangane da batun cewa su ba ’ya’yan Jam’iyyar APC ba ne, ya ce Shugaban Riko na Jam’iyyar ta Kasa, Alhaji Mai Mala Buni shi ya yi masu rajista kafin a ba su aikin “Kuma shi yake da wuka da nama a hannunsa, ya yi mana rajista kafin ya ba mu takarda cewa mu je mu kama aiki.’’

Ya kara da cewa babu wani bambanci a tsakanin wanda ya “shekara hamsin’’ a cikin jam’iyyar da kuma wanda ya shigo a yau.

Matsayin Uwar Jam’iyyar APC ta Kasa

Daya daga cikin manyan abubuwan da Shugaban Riko na Jam’iyyar APC ta Kasa ya mai da hankali a kai a cikin watannin nan, shi ne sasanta rikicin jam’iyyar a bangarori daban-daban da kuma kokarin jawo ’yan hamayya su shiga jam’iyyar.

Ana ganin shi kansa sauya shekar Gwamnan Jihar Zamfara daga PDP zuwa APC, sakamako ne na yunkurin uwar jam’iyyar ta kasa.

To sai dai rigingimun da hakan ya janyo a jihar suna neman mayar da hannun agogo baya.

Dangane da takaddama ta bayabayan nan a jihar, uwar jam’iyyar ta kasa ta ce ba ta saba wa ka’idodjin jam’iyya ba kuma dukkan matakan da aka dauka an yi haka ne domin a samu maslaha.

Malam Salisu Na’inna Dambatta, Daraktan Yada Labarai na Jam’iyyar APC ta Kasa, ya ce kafin a rusa shugabannin jam’iyyar a Jihar Zamfara, sai da aka tuntubi dukkan wadanda suke da ruwada-tsaki, kafin a kafa kwamitin rikon kwarya, bayan Gwamnan ya komo APC.

Ana ganin wannan rigima a matsayin wani babban kalubale ga Jam’iyyar APC a jihar a daidai lokacin da ake tunkarar zaben 2023.

Uwar jam’iyyar ta kasa dai ta ce a karshen watan Yulin nan ne ake sa ran gudanar da tarurrukan shugabannin jam’iyyar a matakan gundumomi a kasar nan.

Daga bisani za a yi na kananan hukumomi da jihohi, sai kuma matakin tarayya.

Manufar hakan, a cewar Dambatta, ita ce a samu zababbun shugabannin jam’iyyar da za su tafiyar da al’amuranta a dukkan matakai.