✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin APC: Shugabanci ya dawo hannun bangaren Buni

An fara sayar da takardun neman tsayawa takara bayan Sakataren APC daga bangaren Buni ya dawo bakin aiki.

Shugabanci a Hedikwatar Jam’iyyar APC ta kasa ya dawo hannun bangaren Shugaban Rikon Jam’iyyar, Mai Mala Buni, bayan mako guda ana tataburzar da ta kai ga rade-radin cewa an tisa keyarsa.

A ranar Talata, Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa daga bangaren Buni, Sanata James John Akpanudoedehe, ya ci gaba da jan ragamar jam’iyyar, kamar yadda ya saba a duk lokacin da Buni ba ya nan.

Tuni kuma ya kaddamar da sayar da takardun neman takarar kujerun shugabancin jam’iyyar, wadanda za a zaba a babban taron jam’iyyar na kasa da zai gudana ranar 26 ga watan Maris da muke ciki.

Wani dan takarar shugabancin jam’iyyar, Saliu Mustapha, wanda shi ne tsohon Mataimakin Shugaban tsohuwar Jam’iyyar CPC na Kasa, ya sayi fom din takarar Shugaban Jam’iyyar APC a kan Naira miliyan 20.

Aminiya ta gano cewa a halin yanzu dai Buni, wanda shi ne Gwamnan Jihar Yobe, yana birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Idan ba a manta ba, bayan tafiyarsa ce wannan sabuwar dambarwar shugabanci ta kunno kai, inda Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello da wadansu jagororin jam’iyyar suka amshe ragamar shugabancinta.

A ranar Juma’a Aminiya ta kawo rahoton cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar da uwar jam’iyyar APC cewa ita ba ta san da zaman Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Sani Bello, a matsayin sabon shugaban rikon jam’iyyar ba.

Tun a ranar Litinin din makon jiya ne Gwamna Bello da wadasu jagororin APC suka yi wa hedikwatar jam’iyyar tsinke, ya jagoranci wani taron gaggawa ya kuma sanar cewa shi ne a matsayin Mukaddashin Shugaban Rikon Jam’iyyar.

A cewarsa, tun kafin ranar ya fara aiki a matsayin mukaddashi, amma ya ce bai san makomar Mai Mala Buni ba — Wanda yake shirin jagorantar gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa kafin lokacin.

Wannan ne ya kawo ce-ce-ku-ce, shin korar Buni aka yi, ko kuma murabus ya yi?

Tun a watan Yunin 2020, Buni, wanda shi ne tsohon Sakataren Jam’iyyar APC na Kasa kafin ya zama gwamna a 2015, yake jagorantar APC, a matsayin riko, yake kuma sasanta bangarorin da ke zaman doya da manja a jam’iyyar tare da shirin gudanar da babban taronta na kasa.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sanar cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, tare da amincewar gwamnonin APC 19  ne ya sa a tsige Buni daga kujerar.

A cewar El-Rufai a lokacin, bakin alkalami ya riga ya bushe, domin sun gano wata manakisa da Buni ya shirya wa jam’iyyar domin hana ta gudanar da babban taron nata da take shirin gudanarwa.

Sai dai kuma, bayan Bello ya aika wa INEC takardar gayyata zuwa taron uwar jam’iyyar domin tattauna tsare-tsaren babban taron jam’iyyar wanda shi ya karbi ragamar jagoranta, INEC din ta ce ita Buni ta sani.

INEC ta kara da cewa Gwamna Bello ba shi da hurumin gayyatar, Sakataren Jam’iyyar na Kasa ko Shugabanta ne kadai suke da matsayin yin hakan.

Amma ranar Talata, kimanin kwana uku bayan Buhari ya yi gargadi kan sa-toka-sa-katsin da ya kunno kai a jam’iyyar, bangaren Buni ya dawo bakin aiki, aka fara sayar da takardun neman tsayawa takarar kujerun shugabancin jam’iyyar ga masu sha’awa.