✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Tsige Buni: Yadda tuggun su El-Rufai ya tashi a tutar babu

Yadda gwamnoni uku suka warware tuggun da su El-Rufai suka shirya na tsige Mai Mala Buni

Ana iya cewa yunkurin bagaren Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na hambarar Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni daga kujerar shugabancin rikon jam’iyyar APC ya tashi a tutar babu.

Sanya bakin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi cewa ita ita Buni ta sani a matsayin shugaban rikon APC, da kuma umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa kada a taba kujerar Buni ta jagorantar jam’iyyar sun yi ciksa ga masu son tsige shi daga kujerarsa.

Kawo yanzu, Buni, wanda tun a watan Yunin 2020 yake jagorantar APC, ya tsallake duk tuggun da bangaren El-Rufai ya shirya na ganin shugabancin jam’iyyar ta fita daga hannunsa.

Aminiya ta gano cewa Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello da Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo da kuma David Umahi na Jihar Ebonyi su ne suka tsaya kai da fata wajen kare Mai Mala Buni, wanda shi ne Gwamnan Jihar Yobe.

Su kuma El-Rufai da Gwamnan Ondo, Oluwarotimi Akeredolu da kuma Gwamnan Neja su ne kan gaba wajen neman kawar da Mai Mala Buni.

Dambarwar kawar da Buni

Yunkurin kawar da Buni ya dauki zafi ne bayan tafiyarsa zuwa birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) domin duba lafiyarsa.

A lokacin ne El-Rufai ya yi ikirarin cewa Shugaba Buhari ya ba wa gwamnonin jam’iyyar umarnin tsige Buni su nada Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya maye gurbinsa.

Sai dai kuma tun bayan hawan Gwamna Bello kujerar a matsayin mukaddashin Buni, kura ta ki lafawa a hedikwatar jam’iyyar.

Buhari ne ya sa mu —El-Rufai

A hirarsa da shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya bayyana cewa Buhari ne ya ba su ikon tsige Mai Mala Buni daga shugabacin rikon APC.

El-Ruafi, wanda ya zargi gwamnonin APC da zura ido har abubuwa suka dagule a jam’iyyar ya ce gwamnoni 19 da wani mataimakin gwamna daya na jam’iyyar sun yi ittifakin awaitar da umarnin na Buhari.

A cewarsa, ragowar gwamnoni ukun ne suka yi ta baza ji-ta-ji-tar cewa ba a tsige Buni ba.

“Buhari ya yi zama da mu (gwamnonin APC), ya ba mu aiki da kuma umarnin kafin ya wuce ha hau helikwaftan da ke jiran shi. A hikimar shugaban kasa, ya san za mu iya.

“Kawai dai  wasunmu sun koma ’yan kallo ne har abubuwa suka lalace haka, saboda tunanin da muke da shi cewa ai idan muka ci zabe, sai mu koma shugabancin jama’a, mu bar gudanar da jam’iyya a hannun wadanda suka lakance shi.

“Amma yanzu ta bayyana karara cewa abin da ba a so zai faru. Jam’iyyar na cikin garari, dole mu yi abin da ya kamata.”

Shi ma a nasa bangare, Gwamna Akeredolu na Jihar Ondo ya bayyana gwamnonin da ke goyon bayan bangaren Buni a matsayin ’yan damfara.

A wata sanarwa da ya fitar, Akeredolu ya zargi Buni da sanya APC a aljihunsa da kuma kokarin yi wa manufar Buhari burum-burum.

A cewar Akeredolu, duk da haka, APC ta tallake abin da ya kira juyin mulkin farar hular da su Buni suka kitsa, saboda son mulkinsu da ya sa suka kirkiro wasu shingaye marasa asali.

Ya ce, “Kafa sabon kwamitin riko da babban taron APC ya zama tilas domin tabbatar da da’ar shugabanci da kuma tafiya tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da doka da oda a cikin jam’iyya.

“Abubuwan da suka faru a jam’iyyarmu a ’yan watannin baya-bayan nan babban abin kunya ne. 

“Ba sai na yi dogon bita ba game da mummunar turbar da Gwamna Mai Mala Buni, tsohon shugaban rikon jam’iyyar, ya yi ba, wanda abin takaici ne ga jam’iyyar.” 

Martanim bangaren Buni

Amma gwamnonin bangaren Buni irin su David Umahi na Jihar Ebonyi, sun yi fito-na-fito da bangaren na El-Rufai, inda ya kekashe kasa cewa babu wanda ya tsige Buni.

Umahi ya kuma bayyana cewa Buni ya sa Gwamna Bello na Jihar Neja ne kawai ya zama mukaddashinsa kafin ya dawo daga duba lafiyarsa a Dubai.

Ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar APC a Abakalili, hedikwatar Jihar Ebonyi, cewa “Shugaban rikon jam’iyya ya je duba lafiyarsa ne a kasar waje kuma muna nan a lokacin da ya sa Gwamnan Neja ya zama mukaddashinsa.

“Idan har za a yi wani canji a jam’iyya za a sanar da ku, amma a halin yanzu babu wani sauyi da aka yi kuma babu wata baraka a jam’iyyar.”

Wasikar Buni

Daga baya Buni ya fitar da wata sanarwa cewa zai dawo daga ganin likita ya ci gaba da jan ragamar jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewa ya ba wa Gwamnan Neja wasikar zama mukaddashinsa har sai ya dawo gida.

Wakilinmu ya samu kwafin wasikar mai dauke da kwanan watan 28 ga Fabrairu, 2022, wadda ta tabbatar cewa Buni da kansa ya nada Gwamna Bello a matsyin mukaddashinsa.

Wasikar ta ce, “Ina sanar da kai cewa daga yau 28 ga Fabrairu, 2022 zan tafi duba lafiyata a Hadaddiyar Daular Larabawa, idan na dawo zan ci gaba da aiki a matsayina.

“A tsawon lokacin, na mika ayyukan ofishina na Shugaban Riko da kuma Kwamitin Babban Taron Jam’iyyar APC a gareka, saboda kwamitin ya samu damar kammala shirye-shirye da jagorantar taron na ranar 26 ga watan Maris, 2022 da ma sauran ayyukan ofishin nawa.

“Ina kira ga duk mambobin APC su bayar da goyon baya ga Gwamna Abubakar Sani Bello na Jihar Neja kamar yadda suka ba ni.”