✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin aure ne matsalar da aka fi kawo wa Hisbah a Kano

Hukumar ta ce daga cikin matsalolin da ake kawo mata kara, rikicin aure ya fi yawa.

Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta ce mutuwar aure da sauran matsalolin auren na daga cikin manyan matsalolin da ake kawo mata a Jihar.

Mukaddashiyar Kwamnandan Hukumar mai kula da sha’anin mata, Malama UmmuKulsum Kassim ce ta bayyana hakan a tattaunawarta da aka yi da ita a cikin shirin ‘Barka da Hantsi’ na gidan rediyon Freedom da ke Kano.

Malama Ummukulsum ta ce, “Rashin daukar ragamar kula da iyali daga bangaren maza na daga cikin abubuwan da ke haddasa wannan matsala.

“Wajibi ne maza su rika taimaka wa mata wajen tarbiyyar ’ya’yansu domin bunkasa rayuwarsu,” a cewar Malam UmmuKulsum

Ta ce matsalolin aure na da yawa, amma idan maza suka duba raunin mata tare da tausaya musu, komai na iya zuwa cikin sauki.

Sai dai ta ja kunnen mata wajen kiyaye hakkokin mazajensu a zamantakewar aure.

Ta kuma bayyana cewa sakaci daga bangaren mata na kawo lalacewar aure da ma tarbiyyar ’ya’yan da aka haifa.

Kwamandar Hisbar, ta shawarci iyaye su dage sosai wajen bai wa ’ya’yansu ilimin addinin Musulunci yadda ya dace domin kyautata rayuwarsu a nan duniya da kuma gobe kiyama.