✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin cikin gida ya hana PDP samun dan takarar Gwamnan Ogun a 2023

Baya ga PDP ma, jam’iyar LP ma ba ta da dan takara a jerin sunayen.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce rikicin cikin gida ne ya sanya ba a ga sunan dan takarar jam’iyar PDP ba a jerin sunayen ’yan takarar Gwamnan Jihar Ogun na karshe da ta fitar ba.

INEC ta ce dalilin hakan shi ne umarnin da kotu na soke zabukan cikin gida na jam’iyyar.

Cikin jerin sunayen da INEC ta fitar, Aminiya ta lura PDP ta zo a lamba ta 21 ne, sai dai babu sunayen ’yan takarar Gwamna da mataimakinsa.

Baya ga PDP ma, jam’iyar LP ma ba ta da dan takara a jerin sunayen.

A ranar Talatar da ta gabata ne dai Babbar Kotun Tarayya da ke Abeokuta, ta yanke hukunci kan karar da ’ya’yan PDP uku suka shigar kan zaben fidda gwanin jam’iyar inda ta soke dukkan zabukan jamiyyar na jihar.