✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun daukar ’yan sanda 10,000 ya shiga sabon rudani

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya na cacar baki da Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda, a yayin da ma'aikata ke shirin fara yajin aikin sai bana…

Rikici kan daukar sabbin kuratan ’yan sanda 10,000 a Najeriya ya kara munana a yayin da ma’aikatan Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda (PSC) ke shirin fara yajin aikin sai bana ta gani.

Ma’aikatan Hukumar za su fara yakin aikin sai abin da hali ya yi daga ranar Litinin, 29 ga watan Agusta da muke ciki bisa zargin Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da yunkurin kwace aikin daukar sabbin ’yan sandan daga hannun hukumarsu.

Suna kuma zargin hukumar gudanarwar PSC da rashin yi musu karin girma da kuma kin tura su zuwa kwasa-kwasai na samun horo.

Rikicin PSC da Rundunar ’Yan Sanda

Wannan kuwa na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ke tsaka da yin ja-in-ja da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya kan wanda ke da alhakin daukar sabbin kuratan ’yan sanda 10,000 da Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarni.

A makon jiya ne Hukumar Kula da Aikin Dan Sandar (PSC) ta fitar sanarwa a jaridu cewa za ta fara daukar kananan ’yan sanda.

Bayan haka ne Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya fitar da tasa sanarwar tare da gargadin ’yan Najeriya su yi watsi da sanarwar ta PSC.

Kasa da awa 24 bayan sanarwar gargadin tasa ga ’yan kasa game da hatsarin neman aikin da PSC ta tallata, sai hukumar ta janye sanarwar da ta fara fitarwa.

Rikicin cikin gida a Hukumar PSC

Ana cikin haka ne a ranar Alhamis gamayyar kungiyar ma’aikatan PSC ta zargi shugabancin hukumar da yamutsa duk wani abu da zai tabbatar da gudanar da aiki cikin nasara da hadin kai a hukumar.

Don haka ta ce, an kai su makura, ba za su hakura ba, kuma daga ranar Litinin mambobinta za su tsunduma yajin aiki sai abin da hali ya yi.

A cewarta, babu abin da zai sa su mayar da wukarsu cikin kube face a biya musu bukatunsu da aka cim-ma yarjejeniya a kai.

Wasikar da gamayyar kungiyoyin ma’aikatan ta aika wa shugaban hukumar,  tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya Musiliu Smith, ta ce za su shiga yajin aikin ne saboda an ki biya musu bukatunsu, tun bayan da suka janye yajin aikin gargadi na kwana uku da suka fara ranar 24 ga watan Janairu, 2022.

“Muna fada da babbar murya cewa hukumar gudanarwar PSC ta ki yin duk abin da zai kawo dorewar fahimtar juna da kyakkyawan yanayin aiki ba.

“Saboda haka za mu ci gaba da gwagwarmaya har sai hakarmu ta cim-ma ruwa — an aiwatar da duk alkawura da muka yi yarjejeniya a kansu.

“A bisa haka ne kungiyar da daukacin ma’aikatan hukumar ke sanar da cewa za su fara yajin aiki sai abin da hali ya yi daga ranar Litinin 29 ga watan Agusta, 2022.”

Wasikar da wakilinmu ya samu ganin kwafinta na dauke da sa hannun Shugaban Gamayyar Kungiyoyin Ma’aikata Reshen PSC, Adoyi Adoyi; Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Gwamnati (NCSU), Abayomi Anthony; Sakataren Kungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati (ASCSN), Yusuf Nasidi da kuma Sakataren NCSU, Remi Ogundeji.

Hakamu ta yi na jin ta bakin Shugaban Hukumar PSC, tsohon Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Musiliu Smith, ba ta cim-ma ruwa ba; Mun kira wayarsa, amma ba ta shiga.

Shi kuma mai magana da yawun hukumar, Ikechukwu Ani, mun kira wayarsa, amma babu wanda ya masa, har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto.