✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Filato: Fulani da Irigwe sun sasanta

Shugabannin Fulani da Irigwe sun yi alkawarin zama lafiya da junansu.

Kabiluna Fulani da Irigwe da suka dade ba sa ga maciji da juna a Karamar Hukumar Bassa ta Jihar Filato sun amince su daina yakar juna.

A wani taron tattaunawar sulhun da aka yi a ranar Alhamis wanda shugabannin addini da na kabilu suka halarta, wakilan shugabannin Fulani da Irigwe a jihar sun amince su daina fada da juna.

A lokacin taron, Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah, reshen Jihar Filato, Alhaji Muhammad Nuru sun rungumi juna cikin fara’a da Cif Daniel Geh, wanda ya wakilci Babban Sarkin Irigwe, Rabaran Ronku Aka, a taron.

Taron, da murya daya, ya yi Allah wadai da kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gabi na a gidajensu, ko a kan hanyoyin da ake tare matafiya ana kai musu hari.

Mahalarta taron da ya gudana a Cibiyar Tattaunawa da Sulhu da kuma Zaman Lafiya (DREP) da ke Jos, sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta dauki duk matakan da suka dace na magance matsalar tsaro da ta dade tana goga wa sunan jihar kashin kaji.

A jawabinsa, Cif Geh ya ce tun shekara aru-aru suke zaman lafiya da makwabtansu Fulani kuma za su ci gaba da yin duk abin da ya dace domin tabbatar da zama lafiya da kawar da fitina a tsakaninsu da makwabtansu da sauran kabilu.

A cewarsa, babu yadda za a yi al’umma ta bunkasa ta samu ci gaban da ake bukata a yanayi na tashin hankali.

A nasa bangare, Nuru ya yaba da fahimtar junan da aka samu a taron, ya mai cewa za su isar da sakon ga mabiyansu.

Ya ce duk da cewa bangarorin sun dade suna zaman doya da manja, amma yanzu sun amince sun rungumi juna su zauna lafiya, kuma Fulani na farin cikin sake ci gaba da zama tare da makwabtansu, kabilar Irigwe.

Rikicin Fulani da Irigwe ya lakume daruruwan rayuka, baya ga dabbobi da amfanini gona da sauran kadarori masu  tarin yawa.

Karuwar matsalar a baya-bayan nan ta kara ta’azzari matsalar tsaron da Jihar Filato ta dade tana fama da ita; duk da matakan da gwamantin jihar ta dauka na magance matsalar a baya, haka ba ta cimma ruwa ba.