✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Hausawa da Yarbawa: Fusatattun matasa sun hana gwamnoni shiga fadar Sarki

Bamu yarda ba dole sai kun fara ziyarar fadar Baale.

Al’ummar Yarbawa da ke zaune a kauyen Sasa, sun hana Gwamnonin Oyo da Ondo shiga cikin fadar Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin.

Fusatattun matasan sun haramta wa Gwamnonin shiga fadar Sarkin ne a yayin da suka kai ziyarar gani da ido zuwa Kasuwar Sasa a ranar Lahadi.

Ziyarar Gwamnonin ta biyo bayan rikicin da ya barke tsakanin Hausawa da Yarbawa a ranar Juma’a, inda aka yi asarar rayuka da kadarori.

Kokarin bayar da hakuri ga wadannan fusatattun mutanen da Kwamishinar ‘yan sanda Ngozi Onadeko da jami’anta suka yi domin su bai wa Gwamnonin hanyar wucewa zuwa fadar Sarkin Sasa ya ci tura.

Jami’an gwamnati sun shafe kusan awa daya suna tattaunawa da wadannan mutane ba tare da samun nasara ba.

Fusatattu mutanen sun rika fadin kalaman cewa “bamu yarda ba dole sai kun fara ziyarar fadar Baale domin bamu yarda da Sarkin Sasa ba.

“Ba ma son ganinshi da jama’arsa a cikin garinmu”, in ji mutanen.

Bayan tattaunawar ce Gwamnoni biyun suka yanke shawarar amincewa da bukatun fusatattun mutanen na cewa fadar Baale (wato mai Unguwa) na Yarbawa ya kamata su ziyarta ba fadar Sarkin Sasa ba.

Shugaban Gwamnoni 6 na Kudu maso Yammacin kasa Gwamna Rotimi Akeredelu na Jihar Ondo tare da mai masaukinsa Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo sun kai ziyara zuwa fadar Baale na Sasa daga bisani suka koma gidan Gwamnati domin yi wa manema labarai bayani a kan wannan matsala.

Kusan dukkan shagunan cikin kasuwar ta Sasa an kona su kurmus bayan gidajen da ke zagaye da kasuwar Sasa wadanda daruruwan al’ummar Hausawa ke zaman haya a cikin su.

Kazalika, kayan miya irinsu tumatir da albasa da atarugu da tattasai basu tsira ba wanda wasu daga cikin Hausawan da suka mallaki irin wannan kaya suka yi bayanin irin asarar da suka yi.

Daruruwan mata da kananan yara da suka samu mafaka a gidan Sarkin Sasa bayan korarsu daga gidaje mallakar yarbawa da Hausawan ke biyan kudin haya
Wani sashe na mata da kananan yara da suka samu mafaka a gidan Sarkin Sasa.