✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin Hijabi: An jikkata mutum 5 a Jihar Kwara

Mabiya addinai sun yi wa juna ruwan duwatsu kan yunkurin hana dalibai sanya hijabi a makarantu

Akalla mutum biyar ne suka ji rauni a rikicin da ya barke tsakanin Musulmai da Kirisoci kan sanya hijabi a makarantu da ya ta da jijiyar wuya a Jihar Kwara.

Wannan ya faru ne bayan umarnin Gwamnatin Jihar ga makarantu 10 da lamarin ya shafa, da su bude a ranar Laraba don ci gaba da gudanar da harkar karatu.

Sai dai umarnin ya bar baya da kura, inda Musulmai da Kiristoci ke ce-ce-ku-ce, har ta kai ga yi wa juna ruwan duwatsu.

Wasu da rikicin ya ritsa da su an hange su jini na malala a jikinsu tun daga kawunansu zuwa wasu sassa na jikinsu.

Rikicin ya fi yin kamari a makarantun Surulere, ECWA, Surulere, da makarantar Oja Iya wadanda duk suke a garin Ilorin, amma jami’an tsaro sun yi kokarin kwantar da wutar rikicin.

Jami’an tsaro suka yi ta harba hayaki mai sanya kwalla, don kawar da cincirindon mutanen da suke yamutsin.

Da take zantawa da Aminiya, Misis Bankole J.A, shugabar makarantar sakandaren Baptist, da ke Surulere ta ce, “Musulmi da Kirista sun yi ta jifar juna da duwatsu, kuma mutane da yawa sun ji rauni.”

Wani malami Musulmi, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce Kirista ne suka tare hanya da safiyar ranar Laraba, inda suka ce ba za su taba bari dalibai su yi amfani da hijabi a makarantunsu ba duk da umarnin da gwamnati da kotu suka bayar.

Sanarwar sake bude makarantun ta fito ne daga wajen Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Ilimi da Ci Gaban Jama’a ta Jihar, Mary Kemi Adeosun a ranar Talata.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Ajayi Okansanmi, ya ce bayan samun rahoton abin da ke faruwa, nan take Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya aike da ’yan sanda, kuma sun yi nasarar kwantar da fitinar.