✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin IPOB: Dillalai sun dakatar da kai albasa Jihohin Kudu maso Gabas

Daukar matakin dai ya biyo bayan kwace tirela biyu na albasar da ake zargin ’yan IPOB da yi.

Kungiyar Dillalai da Masu Samar da Albasa ta Najeriya, OPMAN, ta sanar da dakatar da kai albasar zuwa yankin Kudu maso Gabashin Najeriya saboda abin da ta kira rashin tsaro.

Shugaban kungiyar ta OPMAN na kasa Aliyu Isah ne ya sanar da daukar matakin a ranar Laraba.

Ya ce kungiyar ta dauki matakin ne saboda kwace tirela biyu na mambobinta wanda ake zargin mambobin haramtacciyar Kungiyar nan da ke fafutukar kafa kasar Biyafara ta IPOB da yi.

A makon jiya ne dai ’yan IPOB din suka kwace tirela biyu makare da albasar da aka dauko daga Arewacin Najeriya a Jihar Imo inda suka rabar da ita ga jama’ar gari.

Ko a cikin makon dai sai da ’yan kungiyar suka banka wa wasu manyan motoci guda biyu makare da jarkokin manja sama da 2,500 wuta a Karamar Hukumar Nsukka ta Jihar Enugu, mallakin ’yan kasuwar Galadima Road a Jihar Kano.

Lamarin, a cewar shugabannin kasuwar ya jawo musu tafka asarar kudi sama da Naira miliyan 80.