✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin IPOB: Kungiya ta bukaci matasan Arewa su kai zuciya nesa

Wata kungiyar Arewa, ADSI, ta bukaci matasan yankin da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya, tare da kai zuciya nesa da nuna dattaku…

Wata kungiyar Arewa, ADSI, ta bukaci matasan yankin da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya, tare da kai zuciya nesa da nuna dattaku duba da abubuwan da ke faruwa a Najeriya.

Kungiyar ta yi kiran ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fuskantar barazana da hare-haren haramtacciyar kungiyar IPOB mai neman ballewa domin kafa kasar Biafra, kan cibiyoyin gwamnati da ’yan Arewa a yankin Kudu maso Gabas.

A wata sanarwa dauke da sa hannun Shugabar ADSI, Huraira Musa,  ta ce tana da yakinin wanzuwar zaman lafiya da ci gaban Najeriya su ne kadai ginshikan dorewar kasar.

Ta ce manufar kungiyar ita ce ganin dukkan ’yan Arewa suna gogayya wurin ci gaban yankin da ma Najeriya gaba daya ba tare da la’akari da addini ko siyasa ba.

Ta gargadi matasan yankin da su guji tayar da tarzoma, “ku saurari dattawa da shugabanninmu kuma ku bi doka da oda domin kauce wa shiga duk wani rikici a kowane irin yanayi.

“Hanya mafi kyau domin ci gaban dimokiradiyya ita ce tattaunawar lumana da hakuri da juna a daidai lokacin da ake zaman tankiya da zullumi.

“Babu abin da rikici ke haifar wa illa barna da shiga kunci; sam babu ci gaba a ciki,” inji sanarwar.

Ta kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi duk mai yiwuwa domin kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa wanda shi ne babban aikinta.