✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Jos: An sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Kananan Hukumomi 3

Dokar dai za ta ci gaba da aiki har sai abin da hali ya yi.

Bayan ’yan sa’o’i da kafa dokar hana fita a Kananan Hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu da Bassa, da ke Jihar Filato, yanzu haka Gwamnan Jihar, Simon Lalong ya mayar da dokar zuwa ta sa’o’i 24. 

Matakin na zuwa ne bayan kisan gillar da aka yiwa wasu matafiya su 25 a garin Jos lokacin da suka hanyarsu ta komawa Jihar Ondo bayan halartar taron Musulunci a Bauchi.

Yanzu haka dai Gwamnan Jihar ya mayar da doka zuwa ta sa’o’i 24.

Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar mai dauke da sa hanun Kakakin Gwamnan, Dokta Makut Macham ranar Lahadi.

Sanarwar ta ce Gwamnan ya dauki wannan matakin ne, don ganin an kare lafiya da dukiyoyin al’umma, musamman a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

Sanarwar ta ce dokar za ta fara aiki ne daga karfe 2:00 na ranar Lahadi, har sai abin da hali ya yi.

Sanarwar ta kuma shawarci al’umma da su zauna a gidajensu don ganin an bai wa jami’an tsaro dama wajen dawo da doka da oda.