✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin Jos: Sojoji sun kaddamar da kwamitin zaman lafiya

Ana sa ran kwamitin ya lalubo bakin zaren rikicin da ya addabi Jihar.

Kwamandan rundunar tsaro ta Operation Safe Haven (OPSH), Manjo Janar Ibrahim Ali, a ranar Lahadi ya kaddamar da wani kwamitin hadin gwiwa da zai lalubo bakin zaren rikicin da ke addabar Jihar Filato.

Kwamitin, mai mambobi 36, an dora masa alhakin fito da hanyoyin kawo karshen kai sabbin hare-hare da kuma na ramuwar gayya, musamman tsakanin manoma da makiyaya a Jihar.

Bikin kaddamarwar dai ya gudana ne a hedkwatar rundunar da ke Jos, babban birnin Jihar.

Ana sa ran rahoton kwamitin ya kawo karshen tashin-tashinar da Jihar ta tsinci kanta a ciki, musamman a ’yan kwanakin nan da ya haifar da asarar rayuka da ta dimbin dukiyoyi.

Mambobin kwamitin dai an zabo su ne daga kabilu daban-daban daga Kananan Hukumomin Bassa da Jos ta Kudu da ta Arewa wadanda suke da cikakken sani a kan tushen rikicin da nufin ganin sun yi amfani da shi wajen lalubo bakin zaren.

Da yake jawabi yayin kaddamar da kwamitin, Manjo Janar Ali ya roki mambobin kwamitin da su cire son rai da son zuciya ko nuna bambanci yayin aikin nasu.

Shugaban kwamitin, Robert Rigwe Ashi ya gode wa kwamandan saboda amincewa da su da ya yi har ya dora musu nauyin, inda ya sha alwashin cewa za su ba mara da kunya.

Kwamitin dai na da mako biyu kafin ya mika rahotonsa.