✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin kabilanci: An kone gidaje 30 a Binuwai

Rikicin ya fara ne ranar Asabar da daddare, inda ya ci gaba har wayewar garin Lahadi.

A kalla gidaje 30 ne aka kone sakamakon rikicin kabilancin da ya barke a yankin Yandev tsakanin kabilun Ipav da Mbatur da ke Karamar Hukumar Gboko ta Jihar Binuwai.

Wakilinmu ya gano cewa da lamarin ya faru ne ranar Asabar da daddare, inda ya ci gaba har zuwa wayewar garin ranar Lahadi.

Wani ganau a yankin ya tabbatar da cewa  mutane sun rika guduwa daga yankin sannan motocin matafiya sun kaurace wa hanyar da take zuwa Gboko saboda rikicin.

Kazalika, rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne sakamakon wata takaddama a kan fili tsakanin wasu mutane wadanda tuni suka mayar da wukakensu cikin kube.

Tuni dai gwamnatin Jihar ta shiga lamarin inda ta karbe filin da ake takaddama a kan shi, sannan ta gargadi bangarorin da kada su sake yunkurin amfani da shi ta kowacce fuska.

Bugu da kari tawagar gwamnatin Jihar ta kai ziyarar gani da ido yankin karkashin jagoranci Sakaren gwamnati, Farfesa Toni Ijohor da Mai ba Gwamnan Jihar Shawara kan Harkokin Tsaro, Kanal Paul Hamba (mai ritaya) don kiyasta barnar da rikicin ya haifar.

Tawagar ta kuma tattauna da dukkan masu ruwa da tsaki a rikicin inda ta yi Allah-wadai da su tare da shawartar su da su rungumi zaman lafiya, su kaurace wa filin har sai an cimma matsaya.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, kakakin ’yan sandan jihar, DSP Catherine Anene ba ta amsa kiran tarhon wakilinmu ba don jin ta bakin rundunar a kan rikicin.