✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin kabilanci: Mutum 15 sun mutu a Gombe

Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ne tabbatar da hakan yayin da ya ziyarci yankin.

Rikicin kabilancin da ya tashi a yankunan Nyuwar da Jessu a Karamar Hukumar Balanga ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15 da asara dukiya ta dubban Nairori.

Gwamnan jihar Gombe Muhammad Inuwa Yahaya ne tabbatar da hakan yayin da ya ziyarci yankin da yammacin Talata don ganewa idon sa yadda lamarin ya faru.

Ya ce an shaida masa rasuwar mutum takwas a Jessu mutum bakwai a Nyuwar sai kuma asarar dukiyoyi da kayayyakin abinci na dubban Nairori.

Wasu daga cikin gidajen da aka kona a rikicin na Gombe

“Na ganewa idona wajen ajiyar abincin mutane wato rumbu da dama da aka kone” inji Gwamnan.

Ya kara da cewa, “Za mu dauki mataki na kare sake faruwar hakan nan gaba. Nayi magana da Kwamishinan Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Gyaran Tarbiya don ganin yadda za a kai musu tallafin kayan abinci la’akari da cewa an kone rumbuna baki daya.

Yadda aka kona rumbuna yayin rikicin

“Kafin na nazo nan, na kira takwara na Gwamnan jihar Adamawa munyi magana da shi ya kira Kwamishinan ’Yan Sandan jiharsa da shugaban Lungudawa don ganin an shawo kan lamarin,” inji Gwamnan.

Shi ma sabon Kwamishinan ’Yan sandan jihar ta Gombe, Babatunde Ishola Babaita, cewa ya yi daga jin labarin faruwar rikicin ya tura jami’ansa don kwantar da tarzoma.

Wani dan kabilar Lunguda da ya rasa mahaifinsa, Bafi Tackily, ya ce kisan mahaifin nasa mai kimanin shekaru 80 ta ya gigita shi matuka.

Bafi ya Kuma ce rikicin ya fara ne ranar litinin da misalin karfe tara na dare inda ya zargi abokan rigimar tasu da fito musu daga bayan dutse sannan suka far musu.