Rikicin Mali: Jonathan ya ziyarci Buhari | Aminiya

Rikicin Mali: Jonathan ya ziyarci Buhari

Buhari da Jonathan
Buhari da Jonathan
    Ishaq Isma’il Musa da Muideen Olaniyi

Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa yau Alhamis.

A cewar mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, Jonathan ya tattauna da Buhari dangane da halin da ake ciki a kan rikicin siyasar kasar Mali.

Adesina ya ce za a gudanar da taro na musamman na Kungiyar Kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS a Ghana ranar Lahadi don tattauna matsalolin Mali, yana mai cewa dalilin da ya sa Jonathan, a matsayinsa na jakada na musamman daga kungiyar ECOWAS, ya ziyarci Buhari kenan.

Ya kara da cewa Buhari ya jaddada matsayarsa cewa duk wani mataki da Najeriya za ta dauka kan rikicin siyasar Mali za ta yi shi ne a madadin ECOWAS.

Gabanin ziyarar Jonathan ce Buhari a ranar ta Alhamis dai ya karbi bakuncin wakili na musamman daga shugaban rikon kwarya na Mali, Kanal Asimi Goita, inda Shugaban ya yi alkawarin cewa Najeriya za ta yi bakin kokarinta wajen taimaka wa Mali wajen kawo karshen rikicin.