✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Rikicin manoma da makiyaya ya yi ajalin mutum daya a Kano

Yanzu haka wani kuma mutum daya ya jikkata a yankin

Wani mutum a Karamar Hukumar Minjibir da ke Jihar Kano ya gamu da ajalinsa a sakamakon wani rikici da ya barke tsakanin manoma da makiyaya a yankin.

Malam Idi Lawan, wanda dan uwa ne ga marigayi Sanusi, ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Talatar da ta gabata ce marigayin ya wayi gari ya tarar dabbobin makiyayan sun cinye masa wake a gonarsa hakan ya sa ya je ya yi musu magana, lamarin da ya harzuka makiyayan suka sakar masa kibiya wanda kuma daga bisani rai ya yi halinsa.

Ya ce, “Abin da ya faru shi ne ya wayi gari ya taras dabbobin makiyayan nan sun yi masa barna a gona sun cinye waken da ya shuka. Haka kuma akwai wani yaro shi ma da irin hakan ta kasance gare shi.

“To lokacin da wancan yaron ya je ya yi wa makiyayan magana sai suka yi masa dukan tsiya. To shi kuma marigayin da jin hakan sai ya tafi don yi musu magana. To maganar nan da ya yi musu ita ta harzuka su suka sakar masa kibiya a cinyarsa inda ta yi masa rauni daga bisani kuma ya ce ga garinku nan.”

Malam idi ya ce tuni aka yi wa marigayi Sanusu suttura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Iyalan marigayin sun yi kira ga hukumomi da su bi musu hakkin jinin dan uwan nasu.

Wani mazaunin yankin, Basiru Dauda Kunya ya shaida wa Aminiya cewa tun a bara makiyayan suka fara damun mazauna yankin, hakan ya sa manoman suka gaji suka fara yin magana, lamarin da ya janyo rikicin da har aka rasa rai tare da jikkata wasu.

Basiru Abdullahi shi ne Sarkin Fulani a garin, ya bayyana cewa lokacin da suka ga bakin makiyayan ya zauna da su inda suka nuna cewa ba zama za su yi ba a garin sun zo ne don wurin da suke zama ba a gama cire shinkafa ba, amma cikin makonni biyu za su tashi su koma wurin da suka fito.

“Bayan lokacin ya cika ne sai suka yi mana waya cewa ba za su iya tashi ba saboda har yanzu manoman yankin nasu ba su kammala girbe amfanin gonarsu ba. Ai kuwa ba mu yi aune ba sai muka sami labarin cewa dabbobinsu sun fara yi wa manoma barna har ma rikici ya auku a tsakaninsu. Kun ga tun farko sun karya alkawari sannan kuma suka yi wannan barna”

Guda daga wadanda rikicin ya rutsa da su yayin da yake karbar magani

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce a yanzu haka zaman lafiya ya dawo a yankin kuma suna nan suna gudanar da bincike a kan lamarin”

“Bayan faruwar lamarin mun tura jami’anmu yankin inda tuni abubuwa suka daidaita. Kowa ya ci gaba da harkokinsa kamar yadda aka saba. Haka kuma mun hada kai da Kungiyar Fulani ta Miyetti-Allah don gudanar da bincike kan gaba dayan lamarin”

Aminiya ta samu labarin cewa bayan faruwar rikicin, mazauna yankin sun rufe hanyar garin Kunya, wacce ta yi iyaka da garin Babura na Jihar Jigawa, lamarin da ya janyo tsayawar zirga-zirga na wani dan lokaci kafin daga bisani abubuwa su daidaita.