✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin manoma ya lakume rayuka 10

Akalla mutum 10 ne suka rasa ransu sakamakon wani sabon fada da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a Kudancin kasar Chadi. Wani mai shigar…

Akalla mutum 10 ne suka rasa ransu sakamakon wani sabon fada da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a Kudancin kasar Chadi.

Wani mai shigar da kara a yankin Moundou, birni na biyu mafi girma a kasar, Brahim Ali Kolla ya ce galibin kashe-kashen sun faru ne yayin gudanar da jana’iza.

Ya shaida wa kamfanin dillacin labaru na AFP cewa rikicin ya fara ne lokacin da makiyaya suka yi zargin wata saniyarsu ta bata kuma suka bi diddigi suka gano cewa wata gona na da sa hannu wajen batarta.

Ko da suka tura wakili domin ya tawo da ita sai aka kashe shi, sannan manoman suka biyo makiyayan tare da hallaka su yayin gudanar da jana’izar mamacin.

Rikici da arangama tsakanin manoma da makiyaya masu yawo na kara kamari a yankin Sahel inda aka yawan takaddama kan filaye.

Mai shigar da karar ya ce ko a ranar Alhamis sai da jimillar mutum 10, dukkansu makiyaya suka rasa ransu a garin na Moundou.

Sai dai ya ce tuni aka cafke mutum 43 bisa zargin su da hannu wajen tayar da rikicin, ciki har da dagattai.

Ko a ranar Litinin sai da wani rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar makiyaya uku da manoma takwas a wata arangama a Kudancin kasar.