✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin matsafa ya lakume rayuka 5 a Binuwai da Osun

An an daddatsa wani a rikicin kungiyoyin asiri marasa ga maciji da juna

Wata sa-in-sa da ta barke tsakanin wasu kungiyoyin asiri guda biyu da ba sa ga maciji da juna ta yi sanadiyyar kisan mutane uku a Karamar Hukumar Ogbadibo da ke Jihar Binuwai.

Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne daga bikin murnar zagayowar ranar haihuwar daya daga cikin mambobin kungiyar a Odoba-Otukpa ranar Asabar.

Daga nan ne kuma rikicin ya yi ta fantsama har zuwa yankin Obu-Otukpa a ranar Lahadi, dukkansu a Karamar Hukumar ta Ogbadibo.

Wasu majiyoyi sun shaida wa wakilinmu ta waya cewa an daddatsa wani matashi a yankin Obu, sai kuma wasu biyu daga Odoba, lamarin da ya kawo adadinsu zuwa uku.

Shugaban Karamar Hukumar ta Ogbadibo, Prince Samuel Onu ya tabbatar da faruwar lamarin ga ’yan jarida a Makurdi, inda ya ce yana da alaka da ayyukan kungiyoyin matsafa.

Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar, DSP Catherine Anene ta ce ba a kai rahoton lamarin ga Rundunar ba.

A wani labarin kuma, akalla wasu mutum biyu sun mutu bayan wata taho-mu-gama tsakanin kungiyoyin asiri na Aiye da Eiye da ke Oshogbo, babban birnin Jihar Osun ranar Lahadi.

Matsafan sun rika harbi kan mai uwa da wabi tare da fito da muggan makamai suna farautar jama’a, yayin da kowanne daga cikinsu ke kokarin nuna kwanjinsa.

Ganau sun ce akalla mutum uku ne aka kashe sakamakon rikicin.

Wani mazaunin yankin, Ismaheel Aide, ya ce ya ga lokacin da ’yan sanda ke kokarin kwashe gawarwakin wadanda aka kashe din bayan da wutar rikicin ta lafa daga kan hanya.

To sai dai kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Osun, Yemisi Opalola ta shaida wa Aminiya cewa mutum biyu ne aka kashe ba uku ba.