✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin PDP: Kotu ta yi fatali da karar da aka shigar da Kwankwasiyya a Kano

Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Kano ta yi fatali da karar da aka shigar da tsagin Kwankwasiyya na jam'iyyar PDP

Babbar Kotun Tarayya dake zamanta a Kano ta yi fatali da karar da aka shigar da tsagin Kwankwasiyya na jam’iyyar PDP a jihar a kan tarukan jam’iyyar a matakin Kananan Hukumomi.

Tsagin tsohon Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Aminu Wali ne dai ya shigar da karar yana kalubalantar hana shi shiga zabukan jam’iyyar.

Rahotanni sun nuna cewa tsagin ya nufi kotun ne tun a watan Yunin 2020 yana neman ta soke zaben da aka gudanar na matakin mazabu a ranar 17 ga watan Maris na bana.

Sai dai da take kare kanta, PDP ta ce rikicin na cikin gida ne kuma bai kamata a kai shi gaban kotu ba ba tare da bin dukkan matakan sulhu na cikin gidan jam’iyyar ba.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Lewis Allagoa ya amince da hujjojin jam’iyyar cewa shari’ar ba ta cika sharudda ba saboda an shigar da ita ne kwanaki 85 bayan aikata abin da ake kara a kansa.

Hakan ce ta sa a cewarsa, kotun ta yanke shawarar yin fatali da karar.

Kazalika, Mai Shari’ar ya kuma yi watsi da wasu karin korafe-korafen da wasu mambobin jam’iyyar suka shigar saboda rashin cika ka’ida.

Idan za a iya tuna wa, ko a ‘yan kwanakin nan sai da tsagin na Kwankwasiyyar ya ce ba zai fafata a zabukan kananan hukumomin jihar dake tafe a watan Janairun 2021 ba saboda zargin rashin yin adalci.

To sai dai bangaren jam’iyyar na Aminu Wali ya ce babu abinda zai hana shi shiga zaben mai zuwa.