✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin PDP ya dada yin kamari a Plateau

Rikicin bangaren jam’iyyar PDP reshen jihar Filato na tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ibrahim Nasiru Mantu  da bangaren tsohon gwamnan Jihar Jonah Janga  ya…

Rikicin bangaren jam’iyyar PDP reshen jihar Filato na tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Ibrahim Nasiru Mantu  da bangaren tsohon gwamnan Jihar Jonah Janga  ya dada yin kamari.

Bayan da bangaren Sanata Mantu suka kaddamar da Honarabul Nandom Penap a matsayin sabon shugaban riko na jihar ranar Juma’a a sakatariyar jam’iyyar da ke garin Jos.

Bangaren su Sanata Nasiru Mantu sun bayyana cewa sun rusa shugabannin jam’iyyar tare da kaddamar da shugabannin riko na jam’iyyar ne bisa umarnin kwamitin amintattatu na kasa na jam’iyyar.

Da yake zantawa da manema labarai kan wannan al’amari bayan kaddamar da shugabannin rikon, sabon sakataren riko na jam’iyya na jihar Inginiya Godwin Bendir ya bayyana cewa, sun dauki wannan mataki ne ganin cewa, tsofaffin shugabannin jam’iyyar da suka rushe wa’adin shugabancinsu ya kare tun a ranar Lahadi 10 ga watan Mayu, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar na shekara ta 2017  sashi na 47 [1] ya bayyana.

Ganin wa’adin tsofaffin shugabannin jam’iyyar ya kare shi ne kwamitin amintattu na kasa na jam’iyyar ya bayar da umarni kan a dakatar da dukkan ayyukan jam’iyyar.

Kamar yadda gwamnati ta bayar da umarnin a dakatar da dukkan wasu ayyuka sakamakon halin da ake ciki na annobar coronavirus.

‘’Kwamitin amintattu na kasa na jam’iyyar ya kafa wadannan sababbin shugabannin rikon ne don su kula da jam’iyyar har ya zuwa lokacin da aka sami saukin annobar da ake ciki ta coronavirus daga nan su sanya ranar da za a zo a zabi sababbin shugabannin jam’iyyar’’

A lokacin da aka tuntubi jami’in watsa labaran jam’iyyar ta PDP reshen jihar ta Filato Mista John Akans ya bayyana cewa wadannan mutane da suke iqirarin cewa su sababbin shugabannin riko na PDP ne a Filato, ba ainihin  ’yan jam’iyyar PDP bane.

Ya ce, ’yan jam’iyyar APC ne kuma APC ce take daukar nauyin gudanar da wannan aiki da suke yi.

‘’A yanzu da nake magana suna can suna taro da jam’iyyar APC. Suna son su wargaza jam’iyyar PDP ne kafin su bar jam’iyyar.

A wajen ainihin ’yan jam’iyyarmu ta PDP mun yi nisa wajen yin tarurruka daban-daban don ganin mun warware banbancen da ke tsakaninmu.

Kuma har yanzu mune shugabannin riko na wannan jam’iyya.’’