✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rikicin Sarauta: An kashe mutum 7 a Taraba

Rikicin ya barke ne bayan sauke wani mai unguwa kan zargin jagorantar zanga-zanga

Mutum bakwai sun rasu a rikicin sarauta tsakanin kabilun Ichen da Ndakka da ke Masarautar Bissola a Karamar Hukumar Kurmi ta Jihar Taraba.

Shi dai wannan rikicin sarauta ya fara barkewa ne a ranar Asabar bayan sauke wani mai unguwa dan kabilar Ndakka da Sarkin Bissola, wanda dan kabilar Ichen ne, ya yi.

Aminiya ta gano cewa Sarkin Bissola ya sauke mai unguwar Ndakka ne saboda zargin jagorantar wata zanga-zanga da matasan kabilar ta Ndakka suka gudanar.

Zanga-zangar dai ta rikide zuwa tashin hankali, inda aka kashe mutum bakwai tare da kone-konen gidaje tsakanin bangarorin biyu, kafin daga bisani ’yan sanda su shawo kan lamarin.

Kakakin ’yan sandan jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da aukuwar rikicin, amma ya ce mutum daya ne aka kashe.

Ya ce, “Rikicin sarauta ya barke tsakanin kabilun Ichen da Ndakka kuma an kashe mutum daya, amma dai an shawo kan al’amarin bayan an girke ’yan sandan kwantar da tarzoma.”

Zuwa lokacin hada wannan rahoto, Aminiya ta gano al’amura sun lafa a garin Bissola, hedikwatar masarautar.